Juyin Mulki: Jigon PDP Daniel Bwala Ya Fadawa Tinubu Da ECOWAS Muhimman Abubuwa 9 Kan Sojojin Nijar
- Jigon PDP Daniel Bwala, ya zayyano wasu abubuwa da yake so Tinubu da ECOWAS su fahimta kan rikicin Niger
- Bwala ya ce maido da tsarin dimokuradiyya a jamhuriyar Nijar ba abu ba ne da zai yiwu cikin gaggawa kuma cikin sauƙi ba
- A cewar Bwala, amfani da ƙarfin soji ba shi ba ne abinda ya fi dacewa, zai iya hargitsa nahiyar Afrika
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Abuja - Daniel Bwala, kakakin kwamitin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na jam'iyyar PDP a zaben 2023, ya gargadi Shugaba Bola Tinubu kan rikicin siyasar jamhuriyar Nijar.
Ya ce akwai abubuwa masu muhimmanci da ya kamata Tinubu ya duba kafin afkawa sojojin ƙasar da yaƙin da ƙasashen ECOWAS ke shirin yi.
Ya bayyana hakan ne a wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Twitter da safiyar ranar Laraba, 9 ga watan Agusta.
Juyin Mulkin Nijar: Muhimman Abubuwa 12 Da Suka Faru Tun Lokacin Da Sojoji Suka Kifar Da Gwamnatin Bazoum
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wa'adin da ECOWAS ta bai wa sojojin Nijar
Shugaban Najeriya Bola Tinubu, wanda kuma shi ne shugaban ƙungiyar ECOWAS, ya bai wa sojojin Nijar wa'adin kwanaki bakwai kan su mayar da mulki hannun Bazoum da suka karɓa sannan kuma ya sanya musu takunkumi.
Sai dai sojojin sun yi biris da wa'adin na ECOWAS, inda suka ƙara da ɗaukar wasu tsauraran matakai kan ƙasashen da ba sa goyon bayansu.
Daga ciki akwai yanke duk wata hulɗa ta jakadanci da ƙasashen da ke adawa da su, da kuma sanar da rufe sararin samaniyar ƙasarsu a baya-bayan nan.
Abubuwa 9 da yake so ECOWAS ta sani gameda sojojin Nijar
Ana cikin wannan sa-toka-sa-katsin ne Daniel Bwala ya jero wasu muhimman abubuwa 9 da yake son ECOWAS ta duba kafin ƙaddamar da yaƙi kan sojojin na Nijar.
Yanzu-Yanzu: ECOWAS Ta Sake Sanya Sabbin Takunkunmi Kan Juyin Mulkin Jamhuriyar Nijar, Bayanai Sun Fito
1. Takunkumin da ake ƙaƙabawa sojojin ba zai yi wani tasiri a kansu ba, saboda ba za su rasa wata madogarar ba.
2. Amfani da ƙarfin soji ka iya hargitsa Afrika, wanda hakan zai iya sanadin rasa kujerun shugabannin na ECOWAS.
3. Amfani da diflomasiyya ba wai burga ba ne kawai zai tabbatar da dawowar dimokuraɗiyya a Nijar.
4. Matakan dawo da dimokuraɗiyya a Nijar ka iya ɗaukar shekara ɗaya da watanni shida; saboda dole sai an gudanar da zaɓe.
5. Dole ne shugabannin ƙasashen da ke ƙarƙashin ECOWAS su yi ƙoƙarin gudanar da ingantaccen shugabanci a ƙasashensu domin gudun faɗawa irin halin da Nijar take ciki.
6. Dole ne Afrika ta sauya yadda take alaƙa da ƙasashen Yammacin duniya, yanzu kan mage ya waye.
7. Dole ne masu riƙe da muƙamai na siyasa su kasance masu gaskiya da riƙon amana. Dole ne kuma a riƙa bai wa mutane abinda suka zaɓa a lokutan zaɓe.
8. Dole ne a daidaita rabon arziƙin ƙasa cikin adalci ta yadda kowa zai amfana.
9. Dole ne ECOWAS ta sake yi wa kanta garambawul, ya zamto ta mayar da hankali kan batutuwa na tsaro, kasuwanci da sauran abubuwa na ci gaba.
Rijiyar Lemu ya shawarci ECOWAS kan juyin mulkin Nijar
Legit.ng a baya ta yi rahoto kan shawarar da fitaccen malamin addinin Muslunci, Sheikh Muhammad Sani Rijiyar Lemu ya bai wa Shugaba Tinubu da ECOWAS dangane da juyin mulkin Nijar.
Malamin ya shawarcesu da su bi matakai na sulhu wajen warware rikicin ba wai amfani da ƙarfin soji ba.
Asali: Legit.ng