Jigo a NNPP Ya Mayar Da Martani Ga Masu Neman Kwankwaso Ya Yi Murabus

Jigo a NNPP Ya Mayar Da Martani Ga Masu Neman Kwankwaso Ya Yi Murabus

  • Shugabannin NNPP na jihohi sun buƙaci ɗan takarar shugabancin ƙasa na jam'iyyar, Rabiu Kwankwaso ya yi murabus
  • Sun zargi Kwankwaso da ha'intar jam'iyyar inda suka sha alwashin dakatar da shi idan bai yi murabus ba
  • Biyo bayan wannan 'yar yaƙaddamar ne Legit.ng ta tattauna da wani ɗan takarar majalisa a jam'iyyar NNPP Razaq Aderibigbe

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Ikorodu, Legas - Ɗan takarar kujerar Majalisar Dokokin jiha a mazaɓar Ikorodu a ƙarƙashin jam'iyyar NNPP, Adekunle Razaq Aderibigbe, ya yi kira ga magoyan bayan NNPP da kar su bari wasu masu hayaniya sau ɗauke musu hankali.

Ya bayyana hakan ne a lokacin da yake martani kan masu kira ga ɗan takarar shugabancin ƙasa na jam'iyyar ta NNPP, Rabiu Musa Kwankwaso ya yi murabus.

Jigon NNPP ya kare Kwankwaso
Jigon NNPP ya yi martani ga masu neman Kwankwaso ya yi murabus. Hoto: Rabiu Musa Kwankwaso
Asali: Facebook

An zargi Kwankwaso da kulla alaƙa da jam'iyyar APC

Kara karanta wannan

Jam'iyyar NNPP Ta Fusata, Ta Aike Da Muhimmin Gargadi Ga Shugaban APC Na Kasa, Ganduje

Shugabannin jam'iyyar NNPP na jihohi, sun zargi Kwankwaso da ƙulla wata alaƙa da ta saɓa ƙa'ida da jam'iyyar APC mai mulki.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Sun buƙaci Kwankwaso ya yi murabus da karan kan sa, ko kuma su tsige shige shi kamar yadda The Guardian ta wallafa.

Sun kuma zargi Kwankwaso da kunna wutar rikice -rikicen da aka samu a jam'iyyar a jihohin Najeriya.

Sun ce Kwankwaso na ƙulla wata ƙullalliya a ƙasa don ganin ya amshe jam'iyyar daga hannun masu ita na ainihi

Kwankwaso ba zai siyar da mutuncinsa ba

Da yake mayar da martani kan masu kiran Kwankwaso ya yi murabus, jigon NNPP na Legas, ya ce bai kamata a mayar da hankali kan maganganun na su ba.

Ya shaidawa Legit.ng cewa, jam'iyyar ta daɗe da korar mutanen da ke wannan iƙirarin, wanda a dalilin hakan ne suke son yakito jam'iyyar baki ɗaya

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: ECOWAS Ta Sake Sanya Sabbin Takunkunmi Kan Juyin Mulkin Jamhuriyar Nijar, Bayanai Sun Fito

Ya ƙara da cewa Kwankwaso tsohon ɗan siyasa ne da ya daɗe ana damawa da shi, kuma ba a taɓa samunsa da laifin ha'intar jam'iyyar ba.

A dalilin hakan ne Aderibigbe ke ganin cewa Kwankwaso zai ba mara ɗa kunya, domin kuwa ba zai sayar da mutuncinsa ba.

Jam'iyyar NNPP ta yi wa Ganduje martani mai zafi

Legit.ng a baya ta yi rahoto kan martanin da jam'iyyar NNPP ta yi wa shugaban jam'iyyar APC na ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje.

Jam'iyyar ta ce bai kamata ana haɗa Kwankwaso da Ganduje ba, saboda Kwankwaso ba tsaransa ba ne.

Asali: Legit.ng

Authors:
Deen Dabai avatar

Deen Dabai Zaharaddeen Hamisu marubuci kuma ma'aikacin jarida ne da ke da gogewa wajen iya tantance sahihan labarai da na karya. Ya yi digirinsa a jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Baya ga haka, ya shafe sama da shekaru 5 a bangaren aikin watsa labarai wanda hakan ya bashi gogewa ta musamman a aikin jarida. Za a iya tuntubarsa ta adireshinsa na yanar gizo: deen.dabai@corp.legit.ng