Sunayen Ministocin Tinubu 2 Da Ke Da Matsala Da Shaidar Kammala Bautar Ƙasa NYSC

Sunayen Ministocin Tinubu 2 Da Ke Da Matsala Da Shaidar Kammala Bautar Ƙasa NYSC

Majalisar Dattawan Najeriya ta tabbatar da wasu ministocin Bola Tinubu guda biyu duk da suna da matsala da takardar shaidar kammala yi wa ƙasa hidima wato NYSC.

A ranar Litinin, 7 ga watan Agusta ne shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, ya tabbatar da ministoci 45 cikin 48 da Tinubu ya turowa majalisar.

Duk da dai an ware wasu guda uku da ba a kai ga tabbatar da su ba saboda dalilai na tsaro, majalisar ta tabbatar da waɗannan mutanen biyu da ke da matsala da shaidar NYSC.

Ministoci biyu da ke da matsala da takardar kammala NYSC
Ministocin Tinubu 2 da aka tabbatar duk da suna da matsala da takardar NYSC. Hoto: Bola Ahmed Tinubu, Hannatu Musawa
Asali: Twitter

Ministocin Tinubu 2 da ke da matsala da shaidar kammala NYSC

Majalisar Dattawan ba ta ce komai ba dangane da matsalar shaidar kammala bautar ƙasar da ministocin biyu suke da ita.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Kara karanta wannan

Majalisar Dattawa Ta Fitar Da Sabbin Bayanai Kan El-Rufai Da Sauran Ministocin Tinubu 2 Da Ba a Amince Da Su Ba

Hasali ma, majalisar ta tabbatar da su ba tare da wani ya yi musu wata tambaya dangane da hakan ba.

Waɗannan ministoci da ake ta maganganu kan shaidar kammala NYSC ɗinsu su ne:

1. Olubunmi Tunji-Ojo

Tunji-Ojo dai minista ne da Shugaba Tinubu ya bayar da sunansa daga jihar Ondo. Ya yi ɗan Majalisar Wakilai na tsawon wa'adi biyu kafin samun muƙamin minista.

Tunji-Ojo ya yi iƙirarin cewa ya yi bautar ƙasarsa ne a tsakankanin shekarar 2019 zuwa 2023 kamar yadda Premium Times ta ruwaito.

Sai dai wani ma'aikacin hukumar ta NYSC ya ce hakan da mamaki duba da cewa yana matsayin ɗan Majalisar Wakilai a wannan lokacin.

Akwai ƙarin waɗansu ƙorafe-ƙorafe da suka haɗa da sa hannu da kuma lambar da satifiket ɗin na sa ke ɗauke da ita.

2. Hannatu Musa Musawa

Hannatu Musa Musawa minista ce da Tinubu ya ba da sunanta daga jihar Katsina kuma aka tantance ta duk da matsalar takardar shaidar kammala NYSC.

Kara karanta wannan

MURIC Ta Nemi Bahasi Kan Kin Amincewa Da El-Rufai Mukamin Minista Da Majalisa Ta Yi, Ta Bayyana Dalili

Business Day ta ruwaito cewa, Majalisar Dattawa ta tara ta ƙi amincewa da Hannatu Musawa saboda gaza gabatar da takardar kammala NYSC da ta yi a lokacin.

Sai a wannan lokacin, majalisa ta 10 ta tabbatar da ita ba tare da sake tambayarta batun takardun na NYSC ba.

An samu hargitsi wajen tantance ɗaya daga cikin ministocin Tinubu

Legit.ng a baya ta kawo rahoto kan hargitsin da aka samu a Majalisar Dattawa yayin tantance Festus Keyamo a matsayin minista daga jihar Delta.

Wasu daga cikin sanatocin sun buƙaci a dakatar da tantance Festus Keyamo saboda wasu laifuka da ya aikatawa majalisar a baya.

Keyamo dai ya kasance minista a gwamnatin tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, wanda yanzu kuma za a sake damawa da shi a gwamnatin Tinubu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Deen Dabai avatar

Deen Dabai Zaharaddeen Hamisu marubuci kuma ma'aikacin jarida ne da ke da gogewa wajen iya tantance sahihan labarai da na karya. Ya yi digirinsa a jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Baya ga haka, ya shafe sama da shekaru 5 a bangaren aikin watsa labarai wanda hakan ya bashi gogewa ta musamman a aikin jarida. Za a iya tuntubarsa ta adireshinsa na yanar gizo: deen.dabai@corp.legit.ng