Majalisar Dattawa Ta Fitar Da Sabbin Bayanai Kan El-Rufai Da Sauran Ministocin Da Ba a Amince Da Su Ba

Majalisar Dattawa Ta Fitar Da Sabbin Bayanai Kan El-Rufai Da Sauran Ministocin Da Ba a Amince Da Su Ba

  • Ministoci uku na Shugaba Tinubu da ba a amince da naɗin su ba, akwai yiwuwar sake gayyato su gaban majalisa domin sake tantance su
  • Kakakin majalisar dattawa, Yemi Adaramodu, shi ne ya bayyana hakan kwana ɗaya bayan majalisar ta dakatar da tabbatar da su
  • An dakatar da amincewa da Nasir El-Rufai daga jihar Kaduna, Abubakar Danladi daga jihar Taraba da Stella Okotete daga jihar Delta saboda binciken tsaro

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

FCT, Abuja - Majalisar dattawa ta fitar da sabon bayani dangane da ministoci uku da ba a amince da su ba, Mallam Nasir El-Rufai daga jihar Kaduna, Abubakar Danladi daga jihar Taraba da Stella Okotete daga jihar Delta.

Kakakin majalisar dattawan, Yemi Adaramodu, ya bayyana cewa El-Rufai, Danladi da Okotete ƙila za a iya sake gayyatar su zuwa gaban majalisar domin sake tantance su.

Kara karanta wannan

MURIC Ta Nemi Bahasi Kan Kin Amincewa Da El-Rufai Mukamin Minista Da Majalisa Ta Yi, Ta Bayyana Dalili

Kila El-Rufai, Okotete da Danladi su sake bayyana gaban majalisa
Akwai yiwuwar majalisar dattawa ta sake gayyato su El-Rufai, Okotete da Danladi Hoto: Nasir El-Rufai/Stella Erhuvwuoghene Okotete/Hon Aliyu Usman
Asali: Facebook

Adaramodu ya bayyana hakan ne a yayin wata tattauna da gidan talbijin na Channels Television a shirin su na 'Sunrise Daily' ranar Talata, 8 ga watan Agusta.

El-Rufai, Danladi, Okotete za su jira

Da yake amsa tambaya kan ko majalisar za ta tabbatar da El-Rufai, Dalandi da Okotete, ya bayyana cewa za a amince da su ne da zarar majalisar ta gamsu da rahoton binciken tsaro a kansu, cewar rahoton Vanguard.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A kalamansa:

"Ƙorafin da aka yi a kansu abu ne wanda ake bincike a kansa. Don haka, majalisa na gamsuwa, tabbas idan akwai buƙatar mu sake gayyato su zuwa majalisa domin sake tantance su, haƙiƙa za mu yi hakan."
"Idan ɓangaren tsaro ba su gamsu ba, majalisa ba za ta gamsu ba. Ya danganta da abinda hukumomin tsaro da wanda ya zaɓo su suka ce."

Kara karanta wannan

Abin Da Ya Jawowa El-Rufai, Danladi Da Okotete Samun Tasgaro a Zama Ministoci

A ranar Litinin ne dai majalisar dattawan ta amince da naɗin mutum 45 daga cikin ministocin Shugaba Tinubu.

El-Rufai, Okotete Da Danladi Sun Samu Cikas

A baya rahoto ya zo kan cikas da tsohon gwamnan jihar Kaduna, Mallam Nasir Ahmad El-Rufai, Stella Okotete da Abubakar Danladi, suka samu wajen amincewa su zama ministoci a gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu.

Majalisar dattawa ba ta bayar da amincewarta ba domin su zama ministoci inda ta kafa hujja da cewa, rahoton binciken tsaro da ake gudanarwa a kan su bai kammalu ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng