An Samu Hatsaniya a Majalisa Bayan Sanatan APC Ya Kunyata Takwaransa Kan Yin Shigar Da Ba Ta Dace Ba
- Sanata Idris Karimi na jam'iyyar APC ya kunyata takwaransa na jam'iyyar SDP, Ahmed Wadada bisa ƙin sanya tufafin ɗa ya dace a yayin zaman majalisa
- Karimi, Sanata mai wakiltar Kogi ta Yamma, ya karanto dokar majalisar wacce ta tilasta musu yin shiga wacce ta dace
- Shugaban majalisar dattawa, Sanata Godswill Akpabio, ya tabbatar da dokar da sanatan ya karanto yayin da ake hayaniya a majalisar
FCT, Abuja - An samu ƴar ƙaramar hatsaniya a majalisar dattawa lokacin da Sanata Idris Karimi na jam'iyyar APC ya caccaki Sanata Ahmed Wadada na jam'iyyar SDP bisa yin shigar da ba ta dace ba.
Karimi, Sanata mai wakiltar Kogi ta Yamma ya karanto dokar majalisar wacce tace Sanatoci su halarci zaman majalisar cikin shiga ta kamala sananniya wacce ta dace.
Ya kira Wadada, Sanata mai wakiltar Nasarawa ta Yamma bisa yin shigar da ba ta dace ba a zaman majalisar.
Dalilin da ya sa aka ambato Wadada a zaman majalisa
Sanatan mai wakiltar Kogi ta Yamma sai ya kada baki ya ce:
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
"Sanata Wadada, ba ka yi shiga wacce ta dace ba."
Kalaman da ya yi sun sanya majalisar ta kaure da surutu, amma sai shugaban majalisar dattawan, Sanata Godswill Akpabio, ya shiga tsakani ya tabbatar da dokar da Karimi ya karanto.
Yadda APC ta rasa Wadada a hannun SDP
A lokacin da ake tunkarar zaɓen shugaban ƙasa da na ƴan majalisar tarayya na ranar 25 ga watan Fabrairu, Wadada wanda ɗan majalisar wakilai ne na jam'iyyar APC, ya fice daga jam'iyyar sannan ya koma jam'iyyar SDP.
Wadada ya yi ƙorafi kan sunayen deliget na ƙananan hukumomin Keffi da Nasarawa a lokacin da ake tunkarar zaɓen fidda gwanin jam'iyyar APC na kujerar Sanatan Nasarawa ta Yamma.
Ya samu nasarar samun tikitin takarar sanata na jam'iyyar SDP, inda ya lallasa ɗan takarar sanatan jam'iyyar APC.
Keyamo Ya Samu Tangarda a Majalisa
A wani labarin kuma, Festus Keyamo ya samu tangarɗa a wajen tantance shi a amjalisar dattawa domin zama minista.
Majalisar ta kaure da hayaniya bayan da wasu sanatoci suka buƙaci a dakatar da tantance Keyamo saboda rashin mutunta majalisar a baya.
Asali: Legit.ng