Akpabio Ya Garzaya Fadar Shugaban Kasa Bayan Hayaniya A Majalisa Kan Tanrance Keyamo

Akpabio Ya Garzaya Fadar Shugaban Kasa Bayan Hayaniya A Majalisa Kan Tanrance Keyamo

  • Shugaban majalisar Dattawa, Godswill Akpabio ya runtuma zuwa fadar shugaban kasa bayan hatsaniya a majalisa
  • Zuwan shugaban majalisar bai rasa nasaba da hayaniya da aka samu yayin tantance Festus Keyamo a majalisar
  • Sanata Darlington Nwokocha ya kalubalanci Keyamo da rashin mutunta gayyatar majalisa ta tara lokacin ya na minista

FCT, Abuja - shugaban majalisar Dattawa, Godswill Akpabio ya ruga zuwa fadar shugaban kasa bayan hatsaniya kan tantance Festus Keyamo a majalisar.

An hango Akpabio a fadar da misalin karfe 2:55 bayan tsaida tantancewar zuwa wani lokaci, cewar gidan talabijin na Channels.

Akpabio ya runtuma fadar shugaban kasa bayan samun hargitsi a tantance Keyamo
Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio Ya Garzaya Fadar Shugaban Kasa Bayan Hayaniya A Majalisa Yayin Tantance Keyamo. Hoto: Godswill Akpabio/Festus keyamo.
Asali: Twitter

Duk ba a san hakikanin zuwan shugaban majalisar ba, amma bai rasa nasaba da kalubalantar Festus Keyamo da wani Sanata daga Abia ta Tsakiya ya yi.

Sanata Darlington ya kalubalanci Keyamo kan rashin mutunta majalisa

Kara karanta wannan

An Samu Hatsaniya a Majalisa Bayan Sanatan APC Ya Kunyata Takwaransa Kan Yin Shigar Da Ba Ta Dace Ba, Bidiyon Ya Bayyana

Sanata Darlington Nwokocha ya nemi majalisar da ta dakatar da tantance Keyamo kan wasu korafe-korafe a kansa.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Nwokocha na zargin Keyamo da rashin mutunta majalisa ta tara inda Keyamo ke zargin majalisar da cin hanci yayin da ya ki amsa gayyatar majalisar lokacin da ya ke minista a gwamnatin Buhari.

Korafin Nwokocha ta samu goyon baya daga Sanata Enyinnaya Abaribe da ke wakiltar Abia ta Kudu a majalisar Dattawa.

Akpabio ya dage zaman majalisar zuwa wani lokaci don shawo kan matsalar

Shugaban majalisar, Godswill Akpabio ya bukaci a dage zaman majalisar, amma mafi yawan mambobin majalisar su ka rabu gida biyu kan bukatar shugaban, cewar TheCable.

Majalisar ta shiga rudani bayan bukatar dage zaman yayin da shugaban masu rinjaye a majalisar, Opeyemi Bamidele ya gabatar da bukatar dage zaman inda Akpabio ya tabbatar da hakan.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: ECOWAS Ta Sanar Da Ranar Da Za Ta Sake Zama Don Yanke Hukunci Kan Nijar

Shugaba Tinubu Zai Mika Sunayen Ministoci Ga Majalisar Tarayya Makon Nan

A wani labarin, shugaban kasa Bola Tinubu zai mika jerin sunayen ministoci zuwa majakisa a makon da za mu shiga don fara tantance wadanda su ka samu shiga ciki.

Bayan dogon jira da 'yan Najeriya su ka yi a kan sunayen ministocin, an tabbatar da cewa a makon nan sunayen za su isa majalisa.

Rahotanni sun tabbatar da cewa Tinubu ya dade da shirya sunayen ministocinsa, sai dai an samu 'yan sauye-sauye a sunayen bayan shirya komai.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.