Ayyuka 774,000: FG ta bayyana adadin jihohin da za su fara a yau Lahadi

Ayyuka 774,000: FG ta bayyana adadin jihohin da za su fara a yau Lahadi

- Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa za a fara ayyuka na musamman wanda ta shirya domin matasa a yau 1 ga watan Nuwamba

- Kamar yadda mataimakin ministan kwadago na musamman ya sanar, ya ce sai ranar Juma'a mai zuwa za a kaddamar

- Za a fara ayyukan a jihohi 18 da ke fadin kasar nan kafin a gangara sauran jihohi domin ayyukan na musamman

Ayyuka na musamman na gwamnatin tarayya wanda aka shirya domin daukar matasa 774,000 daga fadin kananan hukumomi 774 a fadin kasar nan zai fara a yau Lahadi kuma za a kaddamar a ranar Juma'a.

Aikin wanda da farko aka ce za a fara shi a ranar daya ga watan Oktoba an mayar da shi daya ga watan Nuwamba bayan karamin ministan kwadago da aikin yi, Festus Keyamo (SAN) ya mika bukatar ga shugaban kasa Muhammadu Buhari a kan dage lokacin fara ayyukan.

Amma kuma, Tunde Moshood, mataimaki na musamman ga karamin ministan kwadagon, ya sanar da jaridar Leadership cewa za a kaddamar da shirin a ranar Juma'a, 6 ga watan Nuwamba.

Ya ce, "Tabbas za a fara. Za a fara a ranar 1 ga watan Nuwamna amma ba zai yuwu a kaddamar da shi a ranar ba."

Ya ce karamin ministan kwadago, Festus Keyamo, zai tabbatar da an fara shirin a ranar Lahadi a jihar Delta.

Jaridar Leadership ta gano cewa za a fara shirin a fadin jihohi 18 a kasar nan amma sauran jihohin sai daga baya.

Da yawa daga cikin wadanda suka samu nasarar shiga shirin sun samu sakon kar ta kwana daga bankuna da kuma kananan hukumominsu.

A daya bangare, masu ruwa da tsaki sun jinjinawa yanayin shirin inda suka ce matukar ba a saka siyasa a ciki ba, zai tabbatar da habakar tattalin arziki.

KU KARANTA: Cire kudi da nayi a asusun bankinka babu izininka hakkina ne - Budurwa ga saurayi

Ayyuka 774,000: FG ta bayyana adadin jihohin da za su fara a yau Lahadi
Ayyuka 774,000: FG ta bayyana adadin jihohin da za su fara a yau Lahadi. Hoto daga @Leadership
Asali: UGC

KU KARANTA: Shari'ar nadin Sarkin Zazzau, artabun da aka yi a kotu tsakanin Iyan Zazzau da sauran wadanda ake kara

A wani labari na daban, wata mata ta rasa ranta a daren Litinin yayin damben kwasar kayan tallafin COVID-19 a ma'ajiyar karamar hukumar Kaura dake Kagoro, Daily Trust ta wallafa haka.

Daily Trust sun bayyana yadda mamaciyar, Esther Mba, wacce take da shekaru a kalla 45 ta rasa ranta sakamakon damben dibar kayan tallafin.

Kamar yadda bayanai suka zo, bata-garin sun fara kwasar kayan abincin ne da misalin karfe 7 na daren Litinin, duk da harbe-harben jami'an tsaro da na 'yan sa kai, amma abin ya ci tura.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel