Ganduje: ‘Dan Takarar Shugaban Kasa a PDP Ya Yi Ƙus-Ƙus da Sabon Shugaban APC
- Abdullahi Umar Ganduje ya sa labule da Anyim Pius Anyim a gidansa da ke birnin tarayya Abuja
- Zuwa yanzu ba a san abin da shugaban na APC ya tattauna da tsohon sakataren gwamnatin kasar ba
- Dr. Ganduje ya sha alwashin karfafa jam’iyya mai mulki yayin da aka gagara gane manufar Anyim
Abuja - A ranar Lahadi, sabon shugaban jam’iyyar APC na kasa, Abdullahi Umar Ganduje ya zanta da Anyim Pius Anyim a gidansa.
Daily Trust da ta fitar da labarin ta tabbatar da Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya karbi bukuncin tsohon sakataren gwamnatin tarayya a jiya.
Cif Anyim Pius Anyim ya na cikin wadanda su ka fara neman takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP a 2023, amma bai samu nasara ba.
Zuwa yanzu ba a tabbatar da abin da ya kai ‘dan siyasar wajen shugaban APC mai-mulki ba, Ganduje ya tabbatar da zaman a shafinsa.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Anyim Pius Anyim zai dawo APC
Wasu su na ganin akwai yiwuwar Sanata Pius Anyim ya sauya-sheka daga PDP musamman ganin take-takensa a ‘yan kwanakin bayan nan.
Za a iya tuna cewa tsohon shugaban majalisar dattawan ya ziyarci Mai girma Bola Ahmed Tinubu a fadar shugaban Najeriya kwanakin baya.
Yayin ziyarar, Olisa Metuh ya na tare da Anyim wanda ya rike matsayin sakataren gwamnatin tarayya a gwamnatin Dr. Goodluck Jonathan.
Da yake zantawa da manema labarai a garin Abuja, ‘dan siyasar ya shaida cewa ya zo Aso Villa ne domin taya Bola Tinubu murnar lashe zabe.
Zuwa yanzu ba a samu labarin makasudin haduwar Anyim da Abdullahi Ganduje wanda ya zama shugaban APC a makon da ya gabata ba.
Anyim ya san Ganduje a PDP
Yayin da Sanata Anyim yake majalisar dattawa, Ganduje ya na mataimakin Gwamna a PDP.
Tsakanin 2011 da 2015 da Anyim ya zama SGF, ‘dan siyasar ya koma mulki a Kano, kafin daga baya shi da Rabiu Kwankwaso su koma APC.
An yi taron APC babu Buhari
A makon da ya gabata ne aka ji labari tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi bayanin dalilin gazawarsa wajen zuwa taron APC.
Malam Garba Shehu ya ce Muhammadu Buhari ya aika da afuwarsa, ya nuna bai iya halarta ba ne saboda wasu alkawura da ya dauka a baya.
Asali: Legit.ng