Ganduje Ya Yi Karin Haske Kan Dalilin Rashin Ganin Sunan Kwankwaso a Cikin Ministocin Tinubu

Ganduje Ya Yi Karin Haske Kan Dalilin Rashin Ganin Sunan Kwankwaso a Cikin Ministocin Tinubu

  • Shugaban jam'iyyar APC na ƙasa ya bayyana dalilin da ya sanya Kwankwaso bai samu shiga cikin jerin sunayen ministocin Tinubu ba
  • Ganduje ya bayyana cewa tun farko Kwankwaso dama azarɓaɓi ya yi wajen cewa zai samu muƙami a gwamnatin Shugaba Tinubu
  • Jama'a da dama sun yi tunanin Kwankwaso zai shiga cikin ministocin Shugaba Tinubu biyo bayan ganin ɗasawar da suka yi bayan zaɓe

Jihar Kano - Shugaban jam'iyyar All Progressives Congress (APC) na ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje, ya bayyana dalilin rashin ganin sunan tsohon gwamnan jihar Kano, Rabiu Musa Kwankwaso cikin jerin sunayen ministocin Tinubu.

A cikin satin da ya gabata ne dai Shugaba Tinubu ya aike da ragowar sunayen mutum 19 ga majalisar dattawa domin tantance su a matsayin ministoci.

Ganduje ya fadi dalilin kin ba Kwankwaso minista
Ganduje ya bayyana dalilin hana Kwankwaso mukamin minista Hoto: Dr Abdullahi Umar Ganduje OFR
Asali: Facebook

An yi ta hasashen cewa sunan Kwankwaso zai fito a cikin rukunin ministocin kashi na biyu, bayan ba a ga sunansa ba a cikin rukunin farko mai ƙunshe da mutum 28.

Kara karanta wannan

Daga Karshe Ganduje Ya Bayyana Dalilin Cire Sunan Maryam Shetty Daga Cikin Ministocin Tinubu

Wannan hasashen ganin sunan Kwankwaso a cikin ministocin Tinubu ya biyo bayan ɗasawar da aka ga yana yi da shugaban ƙasar ne tun bayan da ya lashe zaɓen shugabancin ƙasar nan na ranar 25 ga watan Fabarairu.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Dalilin rashin ganin sunan Kwankwaso cikin ministocin Tinubu

A yayin wata tattaunawa da manema labarai a daren ranar Asabar, 5 ga watan Agusta, a birnin Kano, Ganduje ya yi ƙarin haske kan dalilin da ya sanya babu sunan Kwankwaso a cikin ministocin Tinubu, Daily Trust ta rahoto.

Da aka tambayi Ganduje ko meyasa ba a ga sunan Kwankwaso ba a cikin jerin sunayen ministocin Shugaba Tinubu ba, sai ya kada baki ya ce dama tun farko a bakin Kwankwaso aka fara jin maganar naɗin ba daga wajen Tinubu ba, cewar rahoton Eagle Online.

Kara karanta wannan

"Shugaba Tinubu Ya Fi Sauran Shugabannin Najeriya", Cewar Jigon APC, Ya Bayyana Kwakkwaran Dalili

"Eh da gaske ne Shugaba Tinubu ya yi alƙawarin tafiya da kowa a gwamnatinsa, sannan ya cika wannan alƙawarin. Nyesom Wike daga jam'iyyar PDP an naɗa shi minista."
"Amma shi Kwankwaso tun da farko shi ne ya ce za a ba shi muƙami ba wai shugaban ƙasa ne ya faɗi hakan ba."

Ganduje Ya Yi Wa Kwankwaso Shagube

A wani labarin kuma, shugaban jam'iyyar APC na ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje, ya yi wa tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, shaguɓe.

Ganduje ya yi wa Kwankwaso tayin dawowa APC tun da yanzu shi ne yake riƙe da madafun ikon jam'iyyar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng