Ganduje Ya Bayyana Dalilin Cire Sunan Maryam Shetty a Cikin Sunayen Ministoci

Ganduje Ya Bayyana Dalilin Cire Sunan Maryam Shetty a Cikin Sunayen Ministoci

  • Shugaban jam'iyyar APC na ƙasa ya bayyana dalilan da suka sanya aka sauya sunan Maryam Shetty da na Mariya Bunkure
  • Abdullahi Umar Ganduje ya bayyana cewa ƴan bani na iya da ƴan gutsiri tsoma ne na fadar shugaban ƙasa suka sanya sunanta cikin ministoci
  • Ganduje ya bayyana cewa cece-kucen da aka yi ta yi a soshiyal midiya ya taka rawar gani wajen cire sunan Maryam Shetty a cikin jerin ministoci

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Jihar Kano - Shugaban jam'iyyar All Progressives Congress (APC) na ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje, ya yi magana kan dalilan da suka sanya aka cire sunan Maryam Shetty daga cikin sunayen ministocin da suka fito daga jihar Kano.

A cikin satin da ya gabata ne dai Shugaba Tinubu ya aike wa da majalisar dattawa takardar cire sunan Dr. Maryam Shetty daga cikin ministocin da za a tantance inda ya maye gurbinta da Dr. Mariya Mahmud Bunkure.

Kara karanta wannan

"Shugaba Tinubu Ya Fi Sauran Shugabannin Najeriya", Cewar Jigon APC, Ya Bayyana Kwakkwaran Dalili

Ganduje ya bayyana dalilin cire sunan Maryam Shetty
Ganduje ya bayyana dalilan sauya sunan Maryam Shetty da na Mariya Bunkure Hoto: Dr. Maryam Shetty, Dr. Abdullahi Umar Ganduje OFR
Asali: Twitter

Shugaban jam'iyyar APC na ƙasan a yayin wata tattaunawa da Leadership Hausa, ya bayyana cewa ba da saninsu aka sanya sunan Maryam Shetty ba a cikin jerin ministocin da suka fito daga jihar Kano.

Ganduje baya da masaniya yadda sunan Maryam Shetty ya shiga cikin ministoci

Ganduje ya bayyana cewa wasu ƴan gutsiri tsoma da ƴan bani na iya ne na fadar shugaban ƙasar suka saka sunan Maryam Shetty a cikin sunayen ministocin, ba tare da an tuntuɓe su ba.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

A kalamansa:

"Kasan a fada akwai ƴan bani na iya, kasan a fada akwai ƴan gutsiri tsoma, wannan suna sai dai muka ganshi kawai daga sama. Amma tunda mun san shugaban ƙasa yana da ikon yin hakan, mu kuma mabiyansa ne, kuma mun san a dimokuraɗiyya sai ka bi a hankali, sai ka yi haƙuri, saboda haka sai ba mu ce meyasa aka yi haka ba."

Kara karanta wannan

Ministocin Tinubu: Gaskiya Ta Bayyana Kan Ainihin Dalilin Cire Sunan Maryam Shetty

"Na farko dai ba mu santa sosai ba, bamu ma santa ba, to tunda ba mu santa ba bamu da ma'auni da za mu ce za ta iya wannan aiki ko ba za ta iya ba. To amma inda gizo ke saƙar shi ne batun soshiyal midiya. Soshiyal midiya nan kana zato ka yi abu ba wanda ya sani, wataƙila ma kai da ka yi abun an fika sanin ka yi."
"Soshiyal midiya suka fara fitowa suna cewa wannan mai ta alaƙanta da za ta iya riƙe wannan mulki, kuma yanzu mutanen Kano har ma ta kai irin wannan ce za ta wakilci mutanen Kano. To wannan sai ya kawo damuwa. Kaga damuwar nan ba daga Ganduje ta zo ba, ba daga sauran al'umma ta zo ba, damuwa ta zo daga al'umma waɗanda su ke da hange kan wannan lamari."

Tinubu ya damu kan cece-kucen da ake akan Maryam Shetty

Kara karanta wannan

Bidiyo: Yadda Maryam Shetty Ta Samu Labarin Cire Sunanta a Cikin Majalisa, Abinda Ta Yi Ya Ja Hankali

Ganduje ya bayyana cewa wannan damuwar da aka nuna ta je kunnen shugaban ƙasa, wanda ya tambaye shi ko shi ne ya sanya sunanta, inda ya ce sam baya da masaniya kan yadda aka yi sunanta ya shiga cikin ministocin.

Shugaban na APC ya yi bayanin cewa hakan ya sanya Shugaba Tinubu ya shawarce shi kan sauya sunan Maryam Shetty, inda shi kuma ya bayar da goyon bayan a cire sunanta, domin ba wacce ta fi ta cancanta ta riƙe muƙamin.

Ganduje Sun Yi Wa Maryam Shettt Izgili

A wani labarin kuma, tsohon gwamnan jihar Kano da wasu gungun mata sun yi wa Maryam Shetty izgili bayan an tunɓuke sunanta daga cikin ministoci.

A wani bidiyo an nuna Ganduje da tarin wasu mata na yi tsokaci kan cire sunan Maryam Shetty da maye gurbinta da na Mariya Mahmoud Bunkure.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng