Jigon APC Ya Bayyana Shugaba Tinubu a Matsayin Shugaban Da Ya Fi Sauran Shugabannin Najeriya

Jigon APC Ya Bayyana Shugaba Tinubu a Matsayin Shugaban Da Ya Fi Sauran Shugabannin Najeriya

  • Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu yana cikin watansa na uku akan mulki amma har an bayyana shi a matsayin shugaban da ya fi sauran shugabannin Najeriya
  • Anas Abdullahi Kaura, kakakin tsohon gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle, shi ne ya yi wannan furucin cikin wata sanarwa a ranar Asabar, 5 ga watan Agusta
  • Ya bayyana Shugaba Tinubu a matsayin mai faɗa da cikawa wanda yake mutunta waɗanda suka wahalta masa a lokacin zaɓen shugaban ƙasa na 2023

FCT, Abuja - An bayyana shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu a matsayin shugaban ƙasar da Najeriya ba ta taɓa samun irin sa ba, ƙasa da wata uku da hawansa kan karagar mulki.

Anas Abdullahi Kaura, kakakin tsohon gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle, shi ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa a ranar Asabar, 5 ga watan Agusta.

Kara karanta wannan

Sauƙi Ya Zo: Fadar Shugaban Ƙasa Ta Bayyana Mafi Karancin Albashin da Zata Ƙara Wa Ma'aikata a Najeriya

Hadimin Matawalle ya yaba wa Tinubu
Anas Abdullahi Kaura tare da tsohon gwamna Matawalle Hoto: Anas Abdullahi Kaura
Asali: Facebook

Ya yaba wa Shugaba Tinubu bisa sanya sunan ubangidansa (Matawalle) a cikin jerin sunayen ministocin da zai naɗa.

A kalamansa:

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

"Shugaba Tinubu ya fi sauran shugabannin da Najeriya ta taɓa yi, kuma mutum ne mai cika alƙawari. Ya san mutanen da suka yi aiki dare da rana domin nasararsa, saboda ƙoƙarin Matawalle yankin Arewacin Najeriya ya samar da ƙuri'u mafi yawa, musamman daga jihar Zamfara."
"Idan za ku iya tunawa, Bello Matawalle shi ne Darekta Janar na yaƙin neman zaɓen Ahmed Bola Tinubu/ Shettima a Arewacin Najeriya, sannan kowa ya san ƙoƙarin da ya yi wajen ganin Tinubu ya lashe Arewacin Najeriya, wanda ba za a taɓa mantawa da shi ba."

Ya kuma bayyana Shugaba Tinubu a matsayin wanda ya san masoyansa duba da gudunmawar da Bello Matawalle ya ba shi.

Kara karanta wannan

"Yan Najeriya Suna Farin Ciki da Mulkinka" An Faɗa Wa Shugaba Tinubu Halin da Mutane Ke Ciki

Ya ƙara da cewa al'ummar jihar Zamfara na matuƙar godiya ga Shugaba Tinubu bisa wannan damar da ya ba su, sannan jama'a za su amfana musamman matasa, saboda Matawalle mutum ne mai son ci gaban ƙasa da matasa.

'Yan Najeriya Na Farin Ciki Da Mulkinka, APC Ga Tinubu

A wani labarin kuma, shugabannin jam'iyyar APC sun bayyana wa Shugaba Tinubu cewa ƴan Najeriya na murna da kamun ludayin mulkinsa.

Shugabannin na APC sun bayyana cewa ƴan Najeriya na murna da mulkin Tinubu ne saboda jajircewarsa wajen ɗaukar matakai masu tsauri.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng