Yadda Maryam Shetty Ta Samu Labarin Cire Sunanta Tana Cikin Zauren Majalisa

Yadda Maryam Shetty Ta Samu Labarin Cire Sunanta Tana Cikin Zauren Majalisa

  • Maryam Shetty, ɗaya daga cikin ministocin shugaba Bola Ahmed Tinubu daga Kano ta samu zuwa majalisar dattawa domin tantance wa
  • Sai dai tana cikin majalisar sako ya iso daga shugaba Tinubu cewa ya janye sunanta, ya maye gurbin da wata daban daga Kano
  • Maryam ta bayyana cewa tana cikin zauren majalisa ta samu labari amma duk da haka ta gode wa shugaba Tinubu

FCT Abuja - Rahotanni sun bayyana cewa Maryam Shetty tana cikin zauren majalisar dattawa a lokacin da ta samu labarin cire sunanta daga jerin ministoci.

Maryam Shettima, wacce aka fi sani da suna Maryam Shetty, tana ɗaya daga cikin sunayen ministoci 19 da shugaban ƙasa, Bola Tinubu ya miƙa majalisa ranar Laraba, 2 ga watan Agusta.

Maryam Shetty ta je majalisa.
Yadda Maryam Shetty Ta Samu Labarin Cire Sunanta Tana Cikin Zauren Majalisa Hoto: @maryamshetty
Asali: Twitter

An ce Maryam ta isa zauren majalisar tarayya da ke birnin tarayya Abuja a cikin motar SUV baƙa domin tantance ta amma ta ci karo da labarin cewa an maye gurbinta.

Kara karanta wannan

Jerin Ministoci: Dalilin Da Yasa Tinubu Ya Maye Gurbin Maryam Shetti Da Abokiyar Karatunta Mariya Mahmoud

A wani bidiyo da ke yawo a soshiyal midiya, Maryam ta sanya doguwar riga baƙa da kallabi ja, haka nan kuma ta sanya gilashi a fuskarta, ta isa majalisa tare da rakiyar muƙarrabanta.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

A Bidiyon an ga Maryam Shetty na ɗaukar hotuna da wasu mutane, kafin daga bisani bayan samun labarin cire sunanta, ta hau mota ta bar zauren majalisar.

Legit.ng Hausa ta fahimci cewa sunan Maryam na cikin takardar zaman majalisa na yau Jumu'a, hakan na nufin tana cikin waɗanda za a tantance, amma daga ƙarshe wata daban za'a tantance daga Kano.

Tun da farko, mun kawo muku rahoton cewa shugaban ƙasa Tinubu ya janye sunanta kana ya maye gurbinta da Dakta Maigari Mahmud da Festus Keyamo.

Ko me ya sa aka bari sai da ta je majalisa?

Kara karanta wannan

Kano: Muhimman Abubuwa 5 Da Ba Ku Sani Ba Game Da Maryam Shetty Da Tinubu Ya Sauya Sunanta A Jerin Ministoci

Ɗan takarar gwamnan Kano a inuwar jam'iyyar PRP a zaben 2023, Salisu Tanko Yakasai, ya ce ya samu labarin cire sunan Maryam tun jiya da daddare amma bai san meyasa ba a faɗa mata ba.

Dawisu ya wallafa a shafinsa na tuwita cewa:

"Na samu labari tun jiya da daddare, na yi mamaki da babu wanda ya sanar da ita tun wuri, musamman wanda ya tura sunanta, abu be daɗi ba."

Maryam Shetty Ta Maida Martani Bayan Shugaba Tinubu Ya Maye Gurbinta a Jerin Ministoci

A wani rahoton kuma Maryam Shettima wacce aka fi sani da Maryam Shetty ta yi magana a karon farko bayan shugaban ƙasa, Bola Tinubu ya maye gurbinta.

Lamarin ya haddasa kace nace a kafafen sada zumunta amma Maryam ta ce tana godiya da duk matakin da Tinubu ya ɗauka.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262