Ministoci: Maryam Shetty Ta Maida Martani Bayan Tinubu Ya Maye Gurbinta Daga Kano

Ministoci: Maryam Shetty Ta Maida Martani Bayan Tinubu Ya Maye Gurbinta Daga Kano

  • Maryam Shettima wacce aka fi sani da Maryam Shetty ta yi magana a karon farko bayan shugaban ƙasa, Bola Tinubu ya maye gurbinta
  • Matashiyar na ɗaya daga cikin ministoci 19 da Tinubu ya naɗa amma a ranar Jumu'a ya janye sunanta kana ya maye gurbin da mutum 2
  • Lamarin ya haddasa kace nace a kafafen sada zumunta amma Maryam ta ce tana godiya da duk matakin da Tinubu ya ɗauka

FCT Abuja - Ɗaya daga cikin ministocin da shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya naɗa a rukuni na biyu, Maryam Shettima ta yi magana bayan cire sunanta.

A ɗazu ne shugaban majalisar dattawa, Sanata Godswill Akpabio, ya karanta wasiƙar shugaba Tinubu ta janyen sunan Maryam Shettima wacce aka fi sani da Maryam Shetty.

Maryam Shetty, wacce Tinubu ya maye gurbinta.
Ministoci: Maryam Shetty Ta Maida Martabi Bayan Tinubu Ya Maye Gurbinta Daga Kano Hoto: @Maryamshetty
Asali: Twitter

A sakon shugaban ƙasan, ya maye gurbinta da Dakta Maigari Mahmud daga jihar Kano, sannan kuma ya ƙara maɗa sabon minista, Festus Ƙeyamo.

Kara karanta wannan

Kano: Muhimman Abubuwa 5 Da Ba Ku Sani Ba Game Da Maryam Shetty Da Tinubu Ya Sauya Sunanta A Jerin Ministoci

Rahotanni sun bayyana cewa wannan saƙo ya fito daga bakin Akpabio yayin da majalisar ke ci gaba da aikin tantance ministocin a zamanta na ranar Jumu'a, 4 ga watan Agusta, 2023.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Maryam Shetty ta maida martani kan cire sunanta

Da take martani kan maye gurbinta da shugaban ƙasa ya yi, Maryam Shetty ta bayyana cewa ta rungumi duk wani mataki da Tinubu ya ɗauka kuma ta gode wa Allah.

Ta wallafa a shafinta na Tuwita cewa:

"Yanzu nake samun labari a zauren majalisar dattawa cewa shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya zare sunana ya maye gurbin da Dakta Mairiga Mahmud."
"Ina matuƙar godiya da aminta da duk wani mataki da ya fito daga shugaban ƙasa na."

Matashiyar yar kimanin shekara 44 ta shiga jerin ministocin Tinubu a jerin sunayen mutane 19 da ya aike wa majalisa karo na biyu ranar Laraba, 2 ga watan Agusta.

Kara karanta wannan

Bidiyo: Yadda Maryam Shetty Ta Samu Labarin Cire Sunanta a Cikin Majalisa, Abinda Ta Yi Ya Ja Hankali

Sai dai duk da an yi mamakin ganin sunanta a cikin Ministocin da Tinubu ya ɗauko daga jihar Kano, da yawan 'yan Najeriya musamman mata sun ji daɗin naɗa matashiyar.

Shugaba Tinubu Ya da Aike Sakon Jerin Matakan da Zai Ɗauka Kan Sojojin Nijar Ga Majalisa

A wani rahoton kuma Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya sanar da majalisar tarayya shirin ƙungiyar ECOWAS na ɗaukar matakai kan jamhuriyar Nijar.

Shugaban ya sanar da Majalisar dokokin kasar cewa ECOWAS na shirin daukar matakin soji da sauran takunkumi kan masu juyin mulki a Jamhuriyar Nijar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262