An Taso Tinubu, Ana Neman a Cire Tsohon Gwamna Daga Ministoci Kamar Shetty

An Taso Tinubu, Ana Neman a Cire Tsohon Gwamna Daga Ministoci Kamar Shetty

  • Tsohon Gwamna Bello Matawalle ya na cikin tsofaffin Gwamnonin da za su iya zama Ministoci
  • ‘Dan siyasar zai rike kujerar Ministan taryya idan ‘Yan majalisar dattawa su ka tantance shi a yau
  • An soki Shugaba Bola Tinubu a kan yadda aka bar Matawalle, aka cire sunan Maryam Shetty

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Abuja - Legit.ng Hausa ta lura ganin Muhammad Bello Matawalle a cikin sunayen wadanda za a tantance a majalisa, ya jawo ka-ce-na-ce a Najeriya.

Masu bibiyar shafin sada zumunta na Twitter, sun yi tir da zabo tsofaffin Gwamnonin jihohi, musamman Bello Matawalle da ya yi mulkin Zamfara.

Duk da ya rike Kwamishina a baya, kuma ya taba zama ‘dan majalisa kafin zamansa Gwamna, akwai wadanda su ka soki zabin fitaccen ‘dan siyasar.

Matawalle da Maryam Shetty
Ministoci: Bello Matawalle da Maryam Shetty Hoto: @maryamshetty/OfficialAPCNigeria
Asali: Instagram

Masu murna su na yi, masu bakin ciki su na yi

Kara karanta wannan

Kwankwaso, Abba, Abokan Arziki Sun Tuna da Dadiyata Bayan Shekaru 4 da Bacewa

Magoya baya kamar yadda aka gani a wani bidiyo sun yi farin ciki da ganin sunan Matawalle a jerin wadanda za su zama Ministoci a gwamnati.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Matasa a Twitter kamar Sani Waspapping sun fito karara su na adawa ko da ba daga Zamfara su ka fito ba, su ka ce, ‘dan siyasar bai dace da kujerar ba.

"Ban san Maryam Shetty ko kuwa abin da za ta iya ba, amma Wallahi, na yi cikakken imani zai tafi dacewa da Minista a kan mugun mutum wanda bai cancanta ba, Bello Matawalle.
Idan Shugaban kasa Bola Tinubu yana so ya cire sunan wani a jerin, Bello Matawalle ne."

- Sani Waspapping

A cewar Waspapping tun farko ya so ne a dauko gogaggen mutum kamar Rabiu Kwankwaso ya zama Minista daga Kano, amma babu dalilin cire Shetty.

Kara karanta wannan

Abin da Shugaba Tinubu Ya Fada Mana a Aso Villa Inji Shugabannin ‘Yan Kwadago

Matawalle, Badaru da Bagudu

"Idan za su cire sunan Maryam Shetty, to su yi maza su canza Bello Matawalle, Atiku Bagudu da Badaru Abubakar. Na rantse gara in samu Maryam Shetty a kan Matawalle."

- Umh Manga

Wani mai suna Harmless yake cewa a wadanda Bola Tinubu ya jawo, daga wadanda su ka gaza cin jarrabawar WAEC, sai Dokubo Asari da su Matawalle.

Asiya Rodrigo ta ke tambaya:

"Wani surutu aka yi domin a maye gurbin Matawalle?"

Mahdi Shehu a shafinsa na @shehu_mahdi, ya yi ikirarin akwai zargi a kan tsohon Gwamnan.

Shetty ta shiga sahun marasa sa'a

Ku na da labari Maryam Shetty ta ga samu kuma ta ga rashi bayan an bada sunanta domin zama Minista, sai aka ji an maye gurbinta da wata dabam.

Jama’a sun yabi yadda Shetty ta rungumi kaddara a sakamakon ‘bukulun’ da aka yi mata. Fadar shugaban kasa ba ta bada wani dalilin cire sunata ba.

Kara karanta wannan

Binani, Keyamo, Fashola Da 'Yan Siyasa 10 Da Ba Su Da Rabon Zama Ministoci

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng