Bayan Rasa Minista, Kwankwaso na Fuskantar Barazanar Kora a Jam’iyyar NNPP

Bayan Rasa Minista, Kwankwaso na Fuskantar Barazanar Kora a Jam’iyyar NNPP

  • Wata kungiya ta Shugabannin NNPP ta jefi Rabiu Musa Kwankwaso da zargin laifuffuka iri-iri
  • Kwamared Sunday Oginni ne yake jagorantar kungiyar nan, ya zargi ‘dan takaransu da zagon-kasa ciki har da zargin Kwankwaso da hada kai da Bola Tinubu na APC
  • Ibrahim Danlami Kubau, wanda ya nemi takarar kujerar majalisar tarayya na wakilcin Ikara/Kubau a karkashin NNPP a zaben 2023 ya yi tsokaci kan lamarin

FCT, Abuja - Kungiyar shugabannin jam’iyyar NNPP na reshen jihohi sun bukaci Rabiu Musa Kwankwaso ya rubuta takarda cewa ya yi murabus.

Muddin ‘dan takaran shugaban kasar a zaben 2023 bai yi murabus ba, The Guardian ta ce shugabannin sun yi masa barazanar korarsa daga NNPP.

Zargin da ake yi wa Sanata Rabiu Musa Kwankwaso shi ne ya yi wa jam’iyyarsa zagon-kasa tare da nada marasa gaskiya su jagoranci NWC.

Kara karanta wannan

Kwankwaso, Abba, Abokan Arziki Sun Tuna da Dadiyata Bayan Shekaru 4 da Bacewa

Kwankwaso daga NNPP
Wasu na so a kori Kwankwaso daga NNPP Hoto: @Kk_frontline
Asali: Twitter

Kwankwaso ya ci amanar NNPP a zabe?

Shugabannin na NNPP suna so jagoransu ya yi masu cikakken bayanin dangantakarsa da APC a lokacin zabe da bayan gama takara.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

A cewar shugaban wannan kungiya, Kwamred Sunday Oginni, Sanata Kwankwaso ya haddasa rikicin da ake fama da shi a NNPP a fadin kasar nan.

An rahoto Sunday Oginni ya na zargin tsohon gwamnan da jawo rigima domin karbe jam’iyyar adawar daga hannun ainihin wadanda suka kafa ta.

"Burin Kwankwaso yake gabansa"

Kungiyar shugabannin jihohin ta ce Kwankwaso ya yi amfani da jam’iyyar NNPP a zaben 2023 ne kurum saboda a cigaba da damawa da shi a siyasa.

Kwamred Oginni ya kara da cewa taron da ‘dan takaran na 2023 ya rika yi da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya nuna zagon-kasa ya yi wa jam’iyya.

Kara karanta wannan

Abin da Shugaba Tinubu Ya Fada Mana a Aso Villa Inji Shugabannin ‘Yan Kwadago

An saba tsarin mulkin NNPP

Daily Nigerian ta ce ana zargin Sanata Kwankwaso da yi wa kundin tsarin jam’iyyar hamayyar domin shugabanci ya koma hannun shi da mutanensa.

Sannan kungiyar ta ce ba za ta amince da ruguza shugabannin jam’iyya na Ekiti, Neja, Enugu, Katsina, Ribas da Zamfara da ake ikirarin an yi ba.

Rabiu Musa Kwankwaso da ‘yan NWC ba su taimaka da sisin kobo wajen gina NNPP ba, amma Oginni ya ce an yaudari Boniface Aniebonam a yau.

Dr. Aniebonam shi ne shugaban majalisar amintattu kuma wanda ya kafa jam’iyyar. Oginni ba su goyon bayan shugaban rikon kwarya da su ke mulki.

Silar sabanin da ake samu a jam'iyyar NNPP - Ibrahim Danlami Kubau

Ibrahim Danlami Kubau ya nemi takarar kujerar majalisar tarayya na mazabar Kubau/Ikara a NNPP a zaben 2023, ya fadawa Legit.ng Hausa cewa abubuwa biyu ne suka yi sanadiyyar rikicin cikin gidan.

A cewar Kubau:

Kara karanta wannan

Matawalle, El-Rufai Da Tsofaffin Gwamnonin 3 Da Sunayensu Ya Fito Cikin Ministocin Tinubu Kashi Na Biyu

"A jihohi bakwai da aka dakatar da aka daktar da shugabannin jam'iyya, majalisar NWC ta yi wa kowa adalci."

An zauna da kowa domin jin abubuwan da suka farau kafin zabe da bayan zaben bana, a dalilin haka NWC ta ruguza duka matakan shugabannin.

Su kuma shugabannin kananan hukumomi da na mazabu a gefe guda suna zargin ba a saurare su ba kuma ba a musu adalci ba.

A cewar Danlami Kubau, shugabannin da aka fatattaka suna zargin Rabiu Kwankwaso ne ya yi wa NNPP zagon-kasa, ya hadu da Bola Tinubu.

Ministocin Kano za su tada kura

Kun samu labari magoba bayan Abdullahi Ganduje da Rabiu Kwankwaso ba su ji dadin ganin jerin Ministocin da Bola Tinubu yake shirin nadawa ba.

Zakulo Maryam Shetty da Abdullahi T. Gwarzo da aka yi daga Kano ya zama abin magana bayan an yi tunanin za a dauko shahararrun 'yan siyasa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng