Wike Ya Kulla Abota da Jam'iyyar APC Ne Domin Samun Mafaka, Jiga-Jigai a Ribas

Wike Ya Kulla Abota da Jam'iyyar APC Ne Domin Samun Mafaka, Jiga-Jigai a Ribas

  • Shugabannin APC sun tona asirin tsohon gwamnan Ribas, Nyesom Wike, a daidai lokacin da Tinubu ya naɗa shi minista
  • A wata sanarwa da suka fitar ranar Alhamis, sun ce Wike ya lallaɓa jikin APC ta ƙasa ne domin ceto siyasarsa da ke kan siraɗi
  • Sun kuma bayyana cewa suna da kwararan hujjojin cewa Wike bai taimaki APC ba a zaben shugaban ƙasa na 2023

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Rivers - Wasu jiga-jigan jam'iyyar APC reshen jihar Ribas sun fallasa manufar da ta sanya tsohon gwamnan jihar, Nyesom Wike, ke ɗasawa da jam'iyya mai mulki a matakin ƙasa.

A cewarsu, Wike ya ruga zuwa wurin jam'iyyar APC ne domin ceton siyasarsa wacce alamu suka nuna ta kama hanyar rushewa a jihar Ribas, Punch ta ruwaito.

Tsohon gwamnan Ribas, Nyesom Wike.
Wike Ya Kulla Abota da Jam'iyyar APC Ne Domin Samun Mafaka, Jiga-Jigai a Ribas Hoto: Nyesom Wike
Asali: Twitter

Sun kuma bayyana cewa Wike, tsohon ƙaramin ministan ilimi a Najeriya, bai cancanci yabo ko kaɗan ba game da ci gaban da jam'iyyar APC ta samu a matakin jihar.

Kara karanta wannan

Matawalle, El-Rufai Da Tsofaffin Gwamnonin 3 Da Sunayensu Ya Fito Cikin Ministocin Tinubu Kashi Na Biyu

Hakan na kunshe ne a wata sanarwa da sakataren watsa labaran APC reshen jihar Ribas, Darlington Nwajulu, ya fitar a madadin jagororin jam'iyyar ranar Alhamis.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A cewarsu kafa jam’iyyar APC da ci gaban da aka samu a jihar ya ƙunshi “kokarin da wasu ‘yan uwa masu biyayya, wadanda galibi suka rasa rayukansu a fafutukar kafa ingantaccen tsarin jam’iyyar a Ribas.”

Bai kamata Tinubu ya naɗa Wike minista ba - jagororin APC a Ribas

Shugabannin APC reshen jihar Ribas sun kuma koka kan cewa bai kamata shugaba Bola Tinubu ya saka wa mutumin da a lokacinsa jam'iyyar ta sha fama da hare-hare.

Daily Trust ta rahoto shugabannin na cewa:

“Ci gaban da muka samu daga 2015 zuwa 2019 ya kai kashi 23.8%, wanda ya rufe babban gibin zaben shugaban kasa na 2015. Sai zaben 2023 ya zo da karin kuri’u 80,881, APC ta samu nasara a jihar Ribas."

Kara karanta wannan

Sunayen Ministoci: Jerin Iyayen Gida Masu Tasowa a Siyasance Da Ka Iya Zama Ministocin Tinubu

“Tambayar ita ce, ina taimakon tsohon gwamna Wike? Shin zai iya cewa ya taimaki APC da kuri’u 80,881 kacal, lokacin da ci gaban mu ya fito fili tun daga 2019?"

Dalilin da ya a Wike ya haɗa kai da APC a 2023

Da suke karin haske a cikin sanarwar, shugabannin jam’iyyar sun bayyana cewa Wike ya haɗe da jam’iyyar APC domin ceto rayuwarsa ta siyasa.

"Akwai shaidun da ke nuna cewa Wike bai yi wa APC aiki ba. Da ya gano cewa siyasarsa ta kare, sai ya yanke shawarar jingina da APC, don kawai ya samu damar yi mana fashi."

Jam'iyyar APC Ta Zabi Sabon Shugabanta Na Kasa

A wani rahoton kuma Jam'iyyar APC mai mulki ta zabi tsohon gwamnan Kano, Abdullahi Ganduje a matsayin shugabanta na kasa.

Jam'iyyar ta tabbatar da zaben Ganduje ne a yau Alhamis 3 ga watan Agusta yayin taron masu ruwa da tsaki a birnin tarayya Abuja.

Kara karanta wannan

Emefiele: Peter Obi Ya Dau Zafi Kan Takaddamar Jami'an DSS Da Na Gidan Yari a Kotu, Ya Bayyana Matakin Da Ya Dace a Dauka

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262