Yanzu nan: Shugaba a APC Ya Yi Murabus Yayin da Ganduje Ya Karbi Jam’iyya

Yanzu nan: Shugaba a APC Ya Yi Murabus Yayin da Ganduje Ya Karbi Jam’iyya

  • Ahmed El-Marzuk ya zama na karshe cikin wadanda su ka ajiye kujerar da su ke rike da ita a APC
  • A jiya ne Babban mai ba jam’iyyar APC shawara a kan harkar shari’a ya fice daga majalisar NWC
  • Ana zargin hakan ya biyo bayan sabanin da ya samu da wasu a cikin shugabannin jam’iyya

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Abuja - Babban mai ba jam’iyyar APC shawara a kan harkar shari’a, Ahmed El-Marzuk, ya sauka daga kan kujerarsa a ranar Laraba.

Wani rahoto da aka samu daga Vanguard ya tabbatar da cewa Ahmed El-Marzuk Esq. ya rubuta takardar murabus, ya kuma gabatar a jiya.

Da wannan mataki da ya dauka, Lauyan ya tashi daga zama daya daga cikin ‘yan majalisar NWC.

'Yan APC
Matasan APC a Aso Rock Hoto: @dayoisrael
Asali: Twitter

Meya faru El-Marzuk ya tafi?

Ana tunani El-Marzuk ya sauka daga kujerarsa ne bayan da wasu daga cikin abokan aikinsa a jam’iyyar ta APC mai-ci su ka huro masa wuta.

Kara karanta wannan

Kwankwaso, Abba, Abokan Arziki Sun Tuna da Dadiyata Bayan Shekaru 4 da Bacewa

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Rahoton ya ce za a sanar da wanda zai canje shi kafin a gama zaman majalisar koli ta NEC da ake yi yanzu haka a birnin tarayya da ke Abuja.

Ba mu da cikakken masaniya a game da zargin da ake yi wa Mai bada shawara a kan sha’anin shari’ar, sai dai ana ikirarin akwai laifi a kan shi.

Wannan ne karo na 12 da shugabannin jam’iyya za su zauna tun da aka kafa APC a 2013.

Barista ya bi Adamu, Omisore

Barista El-Marzuk ya dare wannan kujera ne bayan zaben shugabannin na kasa da jam’iyya mai-ci ta shira cikin watan Maris a shekarar 2022.

Kafin shi, shugaban APC na Arewa maso yamma, Salihu Lukman ya yi murabus, wanda Lauyan ya bada shawarar jam’iyya ta ladabatar da shi.

Daga wancan lokaci zuwa yanzu, APC ta rasa shugabanta na kasa, Sanata Abdullahi Adamu da Iyiola Omisore wanda shi ne Sakatarensa a NWC.

Kara karanta wannan

Hotunan Ganduje Sun Kai Hedikwata, Tsohon Gwamnan Kano Ya Shirya Karbar APC

Haka zalika mataimakin shugaban jam’iyya na shiyyar Arewa, Sanata Abubakar Kyari zai sauka daga kujerarsa domin ya zama Ministan tarayya.

Dr. Betta Edu wanda ta ke jagorantar mata a mataki na kasa, za ta ajiye mukaminta a NWC, ita ma ta na cikin wadanda za su zama Ministoci a FEC.

APC ta yi sabon shugaba a Najeriya

Dazu nan rahoto ya zo maku cewa jam'iyyar APC mai mulki ta zabi tsohon gwamnan Kano, Abdullahi Ganduje a matsayin shugabanta a matakin kasa.

APC ta kuma zabi Sanata Ajibola Basiru a matsayin sakataren jam'iyyar na kasa a yau Alhamis, shi ne zai maye gurbin Iyiola Omisore daga Osun.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng