Binani, Keyamo, Fashola da 'Yan Siyasa 10 Da Ba Su Da Rabon Zama Ministoci

Binani, Keyamo, Fashola da 'Yan Siyasa 10 Da Ba Su Da Rabon Zama Ministoci

  • Majalisar Dattawa za ta cigaba da tantance ragowar wanda ake so su zama Ministoci a gwamnatin tarayya
  • Bola Ahmed Tinubu ya aiko sunayen wadanda yake sha’awar su zama Ministocinsa, za a samu mutane 47
  • Shugaban kasa ya jefar da wasu Ministocin baya da wadanda su ka taimaka masa a yakin neman zaben 2023

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Abuja - Rahoton nan ya tattaro sunayen wadanda su ka rasa kujerar Minista tun daga ‘yan takara, jiga-jigan APC da sauran manyan ‘yan siyasa da ake takama da su.

1. Festus Keyamo

Daily Trust ta ce an yi mamakin ganin babu sunan Festus Keyamo SAN a takardar da Femi Gbajabiamila ya gabatar duk da shi ne kakakin yakin zaben APC a 2023.

2. Kayode Fayemi

Kamar dai Festus Keyamo, John Kayode Fayemi yana cikin tsofaffin Ministocin Muhammadu Buhari da aka yi tunanin Bola Tinubu zai tafi da su, ba haka aka yi ba.

Kara karanta wannan

Kwankwaso, Abba, Abokan Arziki Sun Tuna da Dadiyata Bayan Shekaru 4 da Bacewa

Zama Ministoci
Wasu marasa rabon Minista Hoto: FKeyamo
Asali: UGC

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

3. Femi Fani Kayode

Ganin yadda Fani-Kayode ya sauya-sheka daga PDP zuwa APC, ya yi gwagwarmaya a zaben bana, jama’a sun yi tunanin FFK zai koma kan kujerar da ya bari a 2007.

4. Bayo Onanuga

A matsayin Darektan yada labarai a lokacin da Bola Tinubu yake takara, mutane sun hango Bayo Onanuga a matsayin Ministan watsa labarai, bai da wuri a FEC.

5. Ben Ayade

Ben Ayade ya bar PDP zuwa APC da yake Gwamna a Kuros Riba, har yanzu ‘dan siyasar bai samu komai ba duk da tsallakowa da ya yi zuwa jam’iyya mai-ci.

6. James Faleke

Wani makusancin Aso Rock da aka yi ta tunanin za a tantance shi ne Shugaban kwamitin tattalin arziki a majalisa, James Fakele, bai shiga jerin Ministoci ba.

7. Dimeji Bankole

Babu jihar da ta samu Ministoci da yawa kamar Ogun, amma hakan bai sa tsohon shugaban majalisar wakilan tarayya, Rt. Hon. Dimeji Bankole ya dace ce ba.

Kara karanta wannan

Labari Da Dumi-Dumi: Tinubu Ya Nada Atiku, Lalong, Matawalle a Karin Ministoci 19

8. Babatunde Fashola

Wasu sun yi tunanin Tinubu zai dawo da tsohon yaronsa, Babatunde Fashola wanda ya yi Minista a baya, an dauka za a canza masa ofis ne a gwamnatin na.

9. Akinwumi Ambode

Wani tsohon Gwamna da aka sa tsammanin za a ba kujerar shi ne Akinwumi Ambode, ko akalla ya samu takarar idan an zabi Sanata Adetokunbo Abiru.

10. Aisha Dahiru Binani

A hasashen da mu ka yi, Aishatu Dahiru Ahmed za ta samu Minista ganin ta rasa zaben Gwamnan Adamawa ba, ‘yar siyasar ba ta cikin matan da aka dauko.

Ragowar sun hada da Sanata Iyiola Omisore, Rabiu Musa Kwankwaso, Abdullahi Umar Ganduje da tsohon Minsita, Janar Abdulrahman Dambazzau mai ritaya.

Su wanene aka zabo wannan karo?

A sunayen da aka gabatarwa Sanatoci, kun ji labari akwai matashin ‘dan kasuwan nan, Olatunbosun Tijani da tsohon ‘dan majalisa, Dr. Tanko Sununu.

Saidu Alkali Ahmed wanda ya yi Sanata sau uku a Gombe da tsohon Sanatan Neja ta Arewa, Aliyu Sabi Muhammadu su na cikin wadanda za a tantance.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng