Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa Osinbajo Bai Halarci Taron APC Ba, Ya Bada Dalili
- Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Farfesa Yemi Osinbajo, ya faɗi dalilin da ya sa bai halarci taron jam'iyyar APC ba
- Taron wanda aka shirya gudanarwa ranar Laraba, 2 ga watan Agusta, zai tattauna kan rikicin da jam'iyyar ke ciki
- Sai dai tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya aiko da saƙon cewa ba zai samu halartar taron ba, kuma zai ci gaba da zama mamba a jam'iyyar
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Tsohon mataimakin shugaban ƙasa Farfesa Yemi Osibanjo ya bayyana cewa ba zai halarci taron jam’iyyar APC mai mulki da aka shirya yi a ranar Laraba 2 ga watan Agusta ba.
Hakan na ƙunshe ne a wata sanarwa da ya fitar wacce Legit.ng ta gano a shafinsa na Facebook, inda ya ke bayyana cewa ba zai samu halartar taron masu ruwa da tsaki na jam'iyyar ba.
Osinbajo ya ce aiki ne ya yi masa yawa
A cikin sanarwar, Osinbajo ya bayyana cewa rashin halartarsa taron na sa ba ya nufin zai daina hidimtawa jam'iyyar ba ne.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
A cikin wasiƙar ban haƙurin da ya aika zuwa ga shugaban jam'iyyar ta APC na wucin gadi, Osinbajo ya bayyana cewa yanzu haka yana ƙasar waje ne domin wasu aikace-aikace da suka sha ma sa kai.
Ya ce hakan ne ya sa ba zai samu halartar taron jiga-jigan jam'iyyar APC na ranar Larabar ba.
Ya yi alƙawarin halartar taruka na gaba
Osinbajo dai ya soke wasu daga cikin ayyukan da ya ke yi a ƙasashen waje domin samun damar halartar taron jam’iyyar biyu da aka so gudanarwa a baya.
Da yake yi wa jam’iyyar APC fatan alkairi, ya bayyana cewa a shirye ya ci gaba da hidimtawa jam’iyyar, kuma yana fatan halartar taro na gaba.
Ana sa ran cewa manyan jam'iyyar za su magance rikice-rikecen da ke cikinta musamman ma dai rikicin zaɓen sabon Shugaba tun bayan murabus ɗin Adamu Abdullahi.
An sa Wike a kwamitin kamfe na PDP duk da tantance shi matsayin ministan Tinubu
Legit.ng a baya ta yi rahoto kan wani shirgegen kwamitin kamfe na zaɓen jihar Bayelsa da aka sanya Nyesom Wike duk da tantance shi da aka yi a matsayin minista a gwamnatin Tinubu.
Tinubu ya zaɓi Wike don kasancewa ɗaya daga cikin 'yan majalisar ministocinsa duk da kasancewarsa ɗan jam'iyyar PDP.
Asali: Legit.ng