Jerin Sunayen Jihohin Haihuwa Na Ƙarin Ministoci 19 da Tinubu Ya Mika Majalisa

Jerin Sunayen Jihohin Haihuwa Na Ƙarin Ministoci 19 da Tinubu Ya Mika Majalisa

  • Shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasa, Femi Gabajabiamila, ya miƙa jerin sunayen ƙarin ministocin da shugaba Bola Tinubu ya naɗa ga majalisar dattawa
  • Sunayen, waɗanda shugaban majalisar, Sanata Godswill Akpabio ya karanta a zaman ranar Laraba, 2 ga watan Agusta, ya kunshi tsoffin gwamnoni da yan majalisa
  • Wannan karin ministocin ciko ne na ragowar jihohi 11 da shugaban ƙasa bai naɗa minista ko ɗaya ba a rukunin ministocin farko

FCT Abuja -Shugaban Najeriya, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ya miƙa ƙarin ministoci 19 ga majalisar dattawa ranar Laraba, 2 ga watan Agusta, 2023.

Rt. Honorabul Femi Gbajabiamila, shugaban ma'aikatan fadar shugaban ƙasa ne ya kai sunayen ƙarin ministocin ga majalisa domin tantancewa da tabbatar da naɗin su.

Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu.
Jerin Sunayen Jihohin Haihuwa Na Ƙarin Ministoci 19 da Tinubu Ya Mika Majalisa Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Ko kunsan jihohin da sabbin ministocin suka fito?

Mai taimaka wa shugaban ƙasa kan harkokin kafafen sada zumunta na zamani, D. Olusegun, ya wallafa sunayen ƙarin ministoci 19 da kuma jihohinsu na haihuwa a shafinsa na Tuwita.

Kara karanta wannan

Ministocin Tinubu: A Karshe, Akpabio Ya Karanto Sunayen Ragowar Ministocin Da Za a Nada

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Asalin jihohin sabbin ministocin da hadimin shugaban ƙasa ya wallafa a shafinsa ranar Laraba sun hada da;

1. Abdullahi Tijjani Gwarzo (Jihar Kano)

2. HE Simon Bako Lalong (Jihar Filato)

3. HE Muhammad Bello Matawalle (Jihar Zamfara)

4. Tunji Alausa (Jihar Legas)

5. HE Adegboyega Oyetola (Jihar Osun)

6. Uba Maigari Ahmadu (Jihar Taraba)

7. Lola Ade John (Jihar Legas)

8. Dakta Ishak Salako (Jihar Ogun)

9. Sanata Heineken Lolokpobri (Jihar Bayelsa)

10. Dakta Yusuf Tanko Sununu (Jihar Kebbi)

11. Farfesa Tahir Mamman (Jihar Adamawa)

12. Zaphaniah Bitrus Jisalo (Babban birnin tarayya Abuja)

13. Sanata Ibrahim Geidam (Jihar Yobe)

14. Dakta Maryam Shetti (Jihar Kano)

15. Dakta Bosun Tijjani (Jihar Ogun)

16. Shu'aibu Abubakar Audu (Jihar Kogi)

17. Sanata Aliyu Sabi Abdullahi (Jihar Neja)

18. HE Atiku Abubakar Bagudu (Jihar Ƙebbi)

Kara karanta wannan

Sunayen Ministoci: Jerin Iyayen Gida Masu Tasowa a Siyasance Da Ka Iya Zama Ministocin Tinubu

19. Sanata Alƙali Ahmed Sa'idu (Jihar Gombe).

Shugaba Tinubu Ya Gana Shugabannin Ƙungiyoyin Kwadugo a Villa

A wani labarin na daban Bola Ahmed Tinubu ya gana da shugabannin ƙungiyoyin kwadugo a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja ana tsaka da zanga-zanga.

A cewar jagororin yan kwadugon, shugaba Tinubu ya kama hanyar magance buƙatunsu, kuma zasu koma su gaya wa sauran mambobinsu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262