Shugaba Tinubu Ya Dawo Najeria Bayan Kai Ziyara Jamhuriyar Benin
- Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya dawo gida Najeriya bayan kai ziyara Jamhuriyar Benin
- Tinubu ya kai ziyara ga makociyar Najeriya ce don taya su murnan zagayowar ranar ‘yanci karo na 63
- Tinubu ya bar Najeriya da safiyar yau Talata 1 ga watan Agusta tare da wasu gwamnoni shida daga Najeriya
FCT, Abuja - Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya dawo Najeriya daga Cotonou, babban birnin Jamhuriyar Benin.
A yau Talata 1 ga watan Agusta shugaban ya bar Najeriya zuwa taron don taya kasar murnar zagayowar samun 'yanci karo na 63.
An bayyana dawowar shugaban ne ta shafin Twitter na gidan talabijin na kasa, NTA a yau Talata 1 ga watan Agusta.
Shugaba Talon ya gayyaci wasu gwamnonin Najeriya
Bayan Shugaba Tinubu, shugaban kasar Benin, Patrice Talon ya gayyaci gwamnoni guda shida daga Najeriya don taya shi murnar bikin samun ‘yanci.
Gwamnoni shidan su ne wadanda suka hada iyaka da Jamahuriyar Benin kamar su Babajide Sanwo-Olu na jihar Lagos da Dapo Abiodun na Ogun.
Sauran sun hada da Seyi Makinda daga jihar Oyo sai AbdulRahman AbdulRazaq na Kwara da Umar Bago na Niger sai kuma Nasiru Idris na jihar Kebbi.
An bayyana yawan ziyarar da Tinubu ya kai tun bayan hawan shi mulki
Jamhuriyar Benin ita ce ta biyar da Shugaba Bola Tinubu ya ziyarta tun bayan rantsuwar kama mulki da shugaban ya yi a ranar 29 ga watan Mayu a Abuja, Legit.ng ta tattaro.
Rahotanni sun bayyana cewa cire tallafin da Bola Tinubu ya yi, ya shafi tattalin arzikin Jamhuriyar Benin fiye da sauran kasashe.
Shugaban Jamhuriyar Benin a kwanan nan shi ma ya kawo wa Shugaba Bola Tinubu ziyara fadarsa da ke Abuja.
Kwanaki Kadan Da Yin Juyin Mulki A Nijar, Tinubu Ya Tafi Biki A Jamhuriyar Benin
A wani labarin, Shugaba Bola Tinubu ya wuce Jamhuriyar Benin don halartar bikin murnar zagayowar ranar 'yanci karo na 63.
Mai magana da yawun shugaban, Dele Alake shi ya bayyana haka inda ya ce shugaban kasar Benin, Patrice Talon ne ya gayyaci Shugaba Tinubu.
Rahotanni sun tabbatar da cewa Shugaba Talon na Benin ya gayyaci wasu gwamnoni shida daga Najeriya wadanda suka hada da jihohin Lagos da Kebbi da Niger da Ogun da Kwara da kuma Oyo.
Asali: Legit.ng