Tinubu Ya Ce Kokarin Ganin Ya Inganta Rayuwar Kowane Dan Najeriya Ke Hana Shi Bacci
- Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ce inganta lafiya, da jin dadin ‘yan Najeriya yana hana shi bacci cikin dare
- Ya ce ya a tsaye yake dangane da alkawarin da ya dauka na yi wa kowane dan Najeriya aiki tun lokacin da ya karbi rantsuwar fara aiki
- Shugaban ya bayyana hakan ne a ranar Litinin, 31 ga watan Yuli, yayin da yake gabatar da jawabi na kai tsaye ga ‘yan Najeriya
Fadar shugaban kasa, Abuja - Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu, ya bayyana abin da ke hana shi yin bacci dare da rana.
Tinubu ya ce jajircewar da ya yi na ganin ya inganta ilimi, lafiya da jin dadin ‘yan Najeriya, ne ke hana masa yin bacci a kowace rana, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.
Tinubu ya bayyana hakan ne da yammacin ranar Litinin, 31 ga watan Yuli, yayin da yake gabatar da jawabi na kai tsaye ga 'yan Najeriya.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Tinubu ya ce alkawarin da ya dauka yake son cikawa
Tinubu ya bayyana cewa tun lokacin da aka rantsar da shi ya dauki alkawarin yin aiki tukuru ga 'yan Najeriya.
A domin hakan ne shugaban ya kuduri aniyar sauke wannan gagarumin nauyin da ya dauko, wanda ya ce yana da matukar muhimmanci a wurinsa.
A kalamansa:
“Ya ku 'yan uwana ’yan Najeriya, na yi alkawarin yi muku aiki. Yadda zan inganta jin dadin ku da yanayin rayuwarku na da muhimmanci a gare ni kuma shi ne kawai abin da ke hana ni barci dare da rana."
Tinubu ya ba da umarnin samar da motocin bas ga dalibai a matsayin tallafi
Legit.ng ta kawo muku maganar da Shugaba Tinubu ya yi na samar da motocin bas domin jigilar dalibai a manyan makarantun Najeriya.
Hakan na kunshe ne a wata sanarwa da fadar shugaban kasa ta fitar a ranar Litinin, 31 ga watan Yuli, wacce ta bayyana cewa shugaban ya amince da samar da motocin ga jami'o'i, kwalejoji da sauran manyan makarantu.
Shugaba Tinubu na fatan hakan zai ragewa dalibai da iyayensu yawan kudaden da suke kashewa domin zuwa makaranta.
Atiku ya caccaki jawabin da Shugaba Tinubu ya gabatar
Legit.ng a baya ta kawo muku rahoto kan caccakar da dan takarar shugabancin kasa karkashin jam'iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar ya yi wa jawabin da Shugaba Tinubu ya yi.
Atiku ya ce babu komai a cikin jawabin na Tinubu da ya wuce yaudara da kuma bata lokaci.
Asali: Legit.ng