Akpabio Ya Ce Albashin 'Yan Majalisar Dattawa Ba Ya Isarsu Wajen Biyan Bukatunsu
- Shugaban Majalisar Dattawa Godswill Akpabio, ya koka kan yadda albashinsu baya iya biyan bukatun da ke gabansu
- Ya fadi hakan ne yayin da majalisar ke tattaunawa kan yadda za ta dakatar da yajin aikin da kungiyar kwadago ke shirin tsunduma
- Sanata Kawu Sumaila da yake gabatar da kudirin, ya ce tafiya yajin aikin ka iya gurgunta tattalin arzikin kasa
FCT, Abuja – Shugaban Majalisar Dattawan Najeriya, Godswill Akpabio, ya koka kan yadda ‘yan majalisar tarayya ke samun albashi dan kadan.
Akpabio ya ce kudaden da ‘yan majalisar ke samu ba sa isarsu wajen kula da yawan bukatun da suke samu daga mazabunsu, kamar yadda jaridar The Guardian ta ruwaito.
Ya bayyana hakan ne a lokacin da yake mayar da martani kan kudirin da Abdulrahman Kawu Suleiman (NNPP, Kano) ya dauki nauyi, kan bukatar dakatar da kungiyar kwadago ta Najeriya (NLC), daga shiga yajin aikin da ta ke shirin yi.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Yajin aikin zai gurgunta tattalin arziƙin ƙasa
Akpabio ya ce ya aminta cewa jama'a na cikin wani hali tun bayan cire tallafin man fetur, sai dai ya yi kira ga ‘yan Najeriya da su kara hakuri yayin da gwamnati ke tsara matakan rage musu radadin da suke ciki.
Sanata Kawu Sumaila ya ce yajin aikin da ake shirin farawa zai gurgunta tattalin arzikin kasa ta hanyoyi da dama.
Ya ce yajin aikin zai janyo kulle makarantu, masu motocin haya za su daina aiki, zai janyo rufe kasuwanni, asibitoci da sauransu.
Kawu ya ƙara da cewa, yajin aikin zai kuma iya hana masu son zuwa Najeriya domin zuba hannayen jari ko domin huldoɗi na karatu shigowa ƙasar.
Shugaba Tinubu ya ce ƙarin albashi na nan tafe
Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya bayyana cewa ƙarin albashin ma'aikatan Najeriya na nan tafe.
Tinubu ya ce yanzu haka ana tattaunawa don ganin an tsaida mafi ƙarancin albashin da ya kamata a riƙa biyan ma'aikata.
Ya faɗi hakan ne a cikin jawabin da ya gabatar na kai tsaye ga 'yan ƙasa a ranar Litinin, 31 ga watan Yuli.
Fintiri ya ce za su rushe duk gidan da aka samu kayan tallafin jihar Adamawa a ciki
Legit.ng a baya ta yi rahoto kan gargaɗin da gwamnatin jihar Adamawa ta yi ga waɗanda suka saci kayayyakin abinci daga rumbun ajiyar jihar.
Ya bukaci duk waɗanda suka ɗibi kayan su mayar da su zuwa ofishin 'yan sanda mafi kusa da su.
Asali: Legit.ng