Har ‘Yan PDP Sun Koka da Yadda Gwamnansu Ya Ware Musulmai a Rabon Mukamai
- Wata kungiya ta ‘Yan jam’iyyar PDP ta ce gwamnatinta ba ta kama hanyar gaskiya a jihar Filato ba
- A cikin Kwamishinonin da Gwamna Caleb Mutfwang ya nada a Filato, ana tunanin kiristoci ne 99%
- Shugabannin 'Plateau PDP Vanguard for Justice, Equity and Fairness' sun ce akwai bukatar adalci
Plateau - Musulman da su na cikin wadanda aka kafa jam’iyyar PDP da su a jihar Filato, sun yi Allah-wadai da salon mulkin Caleb Mutfwang.
Gwamnan Filato, Caleb Mutfwang yayi rabon mukamai da-dama da ya hau karagar mulki, Daily Trust ta ce ana zargin Kiristoci su ka tashi da 99%.
Ganin Musulmai sun fito sun yi tir da gwamnati, Mai magana da yawun bakin gwamnan Filato ya ce su kwantar da hankali, za a dama da kowa.
‘Yan kungiyar Plateau PDP Vanguard for Justice, Equity and Fairness sun ce sabon Gwamnan da aka rantsar a Mayu bai yi wa Musulmai adalci.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An ci moriyar ganga bayan zabe
Shugabannin kungiyar; Christopher Yusuf da Abubakar Musa sun ce duk gudumuwar da Musulmai su ka ba PDP, an maida su saniyar ware.
Kungiyar siyasar ta yi magana a garin Jos a ranar Litinin, ta ce kiristoci ake ba kusan duk wani mukami har ta kai musulmi daya ya samu Kwamishina.
A cikin kuri’u 60, 000 da PDP ta samu a Jos ta Arewa, ba za a rasa na musulman jam’iyyarmu ba.
Mu na fada da babbar murya jam’iyyar PDP ba ta neman zaman lafiya a Filato da irin nadin mukamanta.
Hakan sam bai dace da manufarmu da burin iyayen gidanmu da su ka kafa jam’iyyarmu ta PDP ba."
- Christopher Yusuf da Abubakar Musa
Kusan haka aka yi a Taraba
A lokacin da Gyang Bere yake kare Gwamnan Filato, yana cewa za a gyara, Legit.ng Hausa ta fahimci musulmai na irin wannan kuka a jihar Taraba.
Kwamishinonin da aka zaba a Taraba su ne: Nicholas Oliver, George Peter, Gideon Nonso, Augustina Godwin, Naomi Agbu, da Sarah Adi.
Har ila yau akwai Joseph Nagombe, Bodia Gbansheya, Habu James, Julius Peter, Saviour Badzoilig, Philister Ibrahim sai Joseph Nagombe.
Premium Times a rahotonta, ta shaida cewa majalisr dokoki ta tantance Mary Sinjen, Daniel Ishaya, Noseh Luka, Joseph, wadanda duk kiristoci ne.
Ragowar Kwamishinonin su ne Aishat Adul-Azzez. Zainabu Usman-Jalingo, Yakubu Maikasuwa, Joshua, Usman Abdullahi da Yakubu Yakubu.
Shugabannin APC a Najeriya
A wani rahoto, kun ji duka wadanda su ka taba zama Shugabannin APC tun da aka kafa ta shekaru goma da su ka wuce, tsofaffin Gwamnoni ne
A tarihin jam’iyyar APC, babu wani Shugaban jam’iyya da ya bar ofis lafiya kalau tun 2018 a 8, a yanzu Abdullahi Umar Ganduje ya na neman kujerar.
Asali: Legit.ng