Majalisa Ta Titsiye Ministan Da Ya Samu Gurbin Karatu a Jami'a Bayan Tsallake Darussa 2 a Jarabawar Sakandire
- Sanata Bello Mohammed ya sha tambayoyi a gaban majalisa bayan ya bayyana a gabanta domin tantance shi ya zama minista
- Sanatocin sun yi masa tambayoyi kan yadda ya samu gurbin karatu a jami'a bayan sakamakon jarabawar sakandirensa bai cika ba
- Mai neman zama ministan ya kare kansa a gaban majalisar inda ya kawo ƙwararan hujjojin da yake da su
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
FCT, Abuja - An yi wa takardun karatun Sanata Bello Muhammad, binciken ƙwaƙwaf ranar Litinin lokacin da ake tantance shi a matsayin ɗaya daga cikin ministocin da Shugaba Tinubu ya naɗa.
Sanatocin sun yi masa tambayoyi kan yadda ya samu gurbin karatu a jami'a da sakamakon gama makarantar sakandire wanda yake ƙunshe kawai da darussa biyu ya tsallake, rahoton Channels tv ya tabbatar.
Sanata Allwell Onyesoh (Rivers ta Gabas), shi ne ya fara masa tambaya, inda ya so sanin ta ya aka yi ya ci gaba da karatu duba da sakamakon da ya samu na gama makarantar sakandire.
"Na duba sakamakon kammala karatun ka, na ga guda ɗaya. Ka zauna jarabawa kan darussa biyar amma ka tsallake guda biyu." A cewar Onyesoh.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
"Ban san ta ya hakan ya faru ba, ina tunanin akwai sauran da ya rage ka kawo. Idan babu ina son ka yi mana bayani yadda ka shiga jami'a da wannan sakamakon."
Abinda ya faru da sauran sakamakon jarabawar sakandirensa
Da yake amsa tambayar, Muhammed ya bayyana cewa yana da wani sakamakon wanda duk ya tsallake darussan amma bai sanya su ba ne a cikin takardun bayanan karatunsa (CV) ba.
"Ina son na tunatar da mai girma sanata duk da ya san cewa da sakamakon sakandire, kamar yadda yake a cikin kundin tsarin mulki, za mu iya tsayawa takarar zaɓe har zuwa matakin shugaban ƙasa." A cewarsa.
"Don haka bana son na cika ku da takardu da yawa. Amma na san waɗannan su ne ƙa'idojin hakan."
Akpabio ya yi masa muhimmin gyara
A daidai wannan gabar ne shugaban majalisar dattawa, Sanata Godswill Akpabio ya yi magana, inda ya yi nuni da bambancin dake tsakanin tsayawa takara da zama minista.
"Kana cewa ka zaɓo abinda kake son gabatarwa ga majalisa. Ka zaɓi sakamakon karatun da zaka kawo wa majalisa saboda kundin tsarin mulki ya yi tanadin cewa sakamakon sakandire shi ne ake buƙata domin tsayawa takara." A cewarsa.
"Ba ka zo nan ba ne domin tsayawa takara, ka zo nan ne domin zama minista a Najeriya. Don haka waɗanne sauran shaidar kammala karatun ka ɓoye? Waɗanne sauran shaidar kammala karatun ne baka sanya a cikin CV ɗin ka ba?"
Muhammed ya yi bayanin cewa, zaman farko da ya yi a jarabawar kammala sakandire, darussa biyu kawai ya tsallake.
"Shugaba Tinubu Ba Zai Yi Dana Sanin Nada Ni Minista Ba", Jawabin Wike Yayin Tantance Shi a Majalisa
Ya kuma ƙara da cewa ya sake zama domin zana wata jarabawar wacce ya yi nasara a dukkanin darussan kawai dai bai sanya ta ba ne a cikin CV ɗin sa.
Akpabio ya kammala da cewa majalisar za ta ba shi lokaci ya kawo sauran shaidar kammala karatun amma ba dole sai ya sake bayyana a gaban majalisar ba.
Majalisa Ta Tantance Ministan Da Ya Fara Karatu Yana Da Shekara 3
A wani labarin kuma, majalisar dattawa ta tantance ministan Shugaba Bola Tinubu wanda ya fara karatu yana da shekara uku a duniya.
Yayin tantance shi ranar Litinin, Farfesa Utsev ya faɗa wa majalisa cewa an haife shi a 1980 kuma ya fara karatun Firamare a 1984.
Asali: Legit.ng