Ministocin Tinubu: Jerin Sunayen Mutane 5 Da Shugaban Kasa zai Iya Zaba Daga Kano

Ministocin Tinubu: Jerin Sunayen Mutane 5 Da Shugaban Kasa zai Iya Zaba Daga Kano

Wani mai sharhi kan al'amuran jama'a, MS Ingawa, ya zayyano sunayen ministoci biyar da Shugaba Bola Ahmed Tinubu zai iya zaba daga jihar Kano.

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

A ranar Alhamis, 28 ga watan Yuli ne Shugaba Tinubu ya mika sunayen ministoci 28 ga Majalisar Dattawa domin tantancewa tare da tabbatar da su.

Sai dai Tinubu bai tura mukami ko guda daya na minista daga jihar Kano da wasu jihohi 10 ba.

Mutane 5 da ake sa ran Tinubu zai ba minista a Kano
Mutane 5 da ake sa ran Tinubu zai iya bai wa mukamin minista daga jihar Kano. Hoto: Dr. Abdullahi Umar Ganduje, Rabiu Musa Kwankwaso, Willy Ibimina Jim-george
Asali: Facebook

Mutane 5 da ake yi wa hasashen samun mukamin minista daga Kano

A wani sakon da ya wallafa a shafinsa na Twitter @MSingawa, ya lissafo jiga-jigan 'yan siyasa biyar da yake ganin Tinubu zai iya zaba a matsayin ministoci daga Kano. Ya lissafo su kamar haka:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kara karanta wannan

Kwankwaso, Jerin Mutum 10 da Za a Saurari Sunayensu a Sahun Karshe na Ministoci

1. Injiniya Rabiu Musa Kwankwaso - Dan takarar shugabancin kasa karkashin jam'iyyar NNPP

2. Abdullahi T Gwarzo - Tsohon mataimakin gwamnan jihar Kano a lokacin Malam Ibrahim Shekarau

3. Rabiu Sulaiman Bichi - Tsohon sakataren gwamnatin Kano a lokacin Kwankwaso

4. Nasiru Yusuf Gawuna - Tsohon mataimakin gwamnan jihar Kano, kuma dan takarar gwamnan APC a jihar Kano

5. Abdullahi Umar Ganduje - Tsohon gwamnan jihar Kano

Abinda ya kawo jan kafa wajen bayyana ministan Kano

Ingawa ya kuma bayyana cewa Shugaba Tinubu ya jinkirta zabar minista daga Kano domin warware matsalar shugabancin jam’iyyar APC bayan murabus din Sanata Abdullahi Adamu.

Legit.ng ta samu cewa, tsohon gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje ka iya zama sabon shugaban jam'iyyar APC na kasa.

Wannan ne ainihin dalilin da ake ganin ya janyo jinkiri wajen bayyana sunan minista daga jihar Kano.

Sai dai MS Ingawa a nasa hasashen yana ganin cewa ba dole ba ne jihar Kano ta iya samun guraben ministoci biyu ba tunda jihar Katsina da ke shiyya daya da ita ta riga da ta samu.

Kara karanta wannan

Ganduje da Tsofaffin Gwamnoni 7 da Tinubu Ya Watsar Wajen Rabon Mukaman Minista

Amma idan kuma Tinubu ya bayar da guraben mutane biyu matsayin ministoci daga jihar Kano, Ingawa yana ganin cewa za a bai wa Kwankwaso da kuma mutum daya daga tsagin Ganduje.

Matasa da matan jam'iyyar APC sun nemi Tinubu ya bai wa Boss Mustapha shugabancin APC

Legit.ng a baya ta yi rahoto kan bukatar kungiyar matasa da mata na jam'iyyar APC ga Shugaba Tinubu, kan ya jingine tsohon gwamnan Kano Abdullahi Ganduje, ya dauko Boss Mustapha domin ba shi shugabancin jam'iyyar APC.

Sun bayyana cewa jam'iyyar a halin da take ciki a yanzu, ta fi bukatar gogaggun mutane da suka san harkokin shugabanci irinsu Boss Mustapha.

Asali: Legit.ng

Authors:
Deen Dabai avatar

Deen Dabai Zaharaddeen Hamisu marubuci kuma ma'aikacin jarida ne da ke da gogewa wajen iya tantance sahihan labarai da na karya. Ya yi digirinsa a jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Baya ga haka, ya shafe sama da shekaru 5 a bangaren aikin watsa labarai wanda hakan ya bashi gogewa ta musamman a aikin jarida. Za a iya tuntubarsa ta adireshinsa na yanar gizo: deen.dabai@corp.legit.ng