Wike Ya Shiga Rudani Tun Lokacin Da Tinubu Ya Nada Shi Minista

Wike Ya Shiga Rudani Tun Lokacin Da Tinubu Ya Nada Shi Minista

  • An rahoto cewa Nyesom Wike na fuskantar matsin lamba tun bayan nada shi minista da Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu ya yi
  • Shugaban kasa Tinubu ya mika sunan Wike da wasu mutane 27 gaban majalisar dattawa domin a tantance su da tabbatar da su a ranar Alhamis, 27 ga watan Yuli
  • An rahoto cewa rudanin da Wike ya shiga yana da nasaba da tsoffin bidiyoyinsa, inda ya ce baya so ya zama minista sannan ya bayyana APC a matsayin mai fama da cutar kansa

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

An rahoto cewa tsohon gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike, yana cikin rudani sosai sannan yana fuskantar matsin lamba tun bayan mika sunansa da Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya yi cikin jerin ministocinsa a ranar Alhamis, 27 ga watan Yuli.

Kamar yadda jaridar ThisDay ta rahoto, Wike na kuma fuskantar matsin lamba yayin da tsoffin bidiyoyinsa yana shan alwashin kin karbar mukamin minista ko komawa jam'iyyar All Progressives Congress (APC) suka ci gaba da yaduwa a soshiyal midiya.

Kara karanta wannan

“Aikin Nan Akwai Hatsari Sosai”: Mai POS Ta Fashe Da Kuka Bayan Ta Karbi Jabun N100K Daga Kwastoma, Bidiyon Ya Yadu

Tsohon gwamnan Ribas, Nyesom Wike na tsaka mai wuya
Wike Ya Shiga Rudani Tun Lokacin Da Tinubu Ya Nada Shi Minista Hoto: Nyesom Wike
Asali: Facebook

A wani bidiyon, Wike ya bayyana APC a matsayin jam’iyyar da ke fama da cutar kansa a mataki na hudu wanda shima yana nan yana yawo a yanzu.

A lokacin kaddamar da masaukin manyan baki a filin jirgin sama na Port Harcourt, Omagwa, Wike ya bayyana karara cewa ba zai zama minista daga jihar Ribas ba.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A yayin da ake ci gaba da diramar siyasa, mambobin jam’iyyar PDP da masu lura da al’amuran siyasa sun zuba ido don ganin yadda Wike zai amshi tayin da aka yi masa na zama minista.

Idan Wike ya amince da mukamin ministan, hakan zai baiwa PDP damar tsige shi daga jam’iyyar, wanda da yawa ke bayyanawa a cikin PDP a matsayin wanda ya wuce gona da iri kuma mai riya.

"Muna fatan zai amshi tayin kuma wannan zai ba jam'iyyar damar fara duba yadda za ta sauya abuuwa da zaran an yi watsi da karar da jam'iyyar ta shigar kotun zaben shugaban kasa.

Kara karanta wannan

Zababbun Ministocin Tinubu: PDP Ta Bayyana Lokacin Da Za Ta Yanke Hukunci Kan Makomar Wike

"Ba zai iya zama minista a gwamnatin APC ba sannan ya ci gaba da zama dan PDP. Eh, ya samu umurni daga kotu wanda ya hana a dakatar da shi, amma yanzu ba zai iya zubarwa sannan ya kwashe daidai ba."

Hakazalika, ana sanya ran PDP za ta yanke hukunci a kansa a gobe. Da yake bayyana hakan ga jaridar ThisDay wani mamba a kwamitin aiki na jam'iyyar (NWC) ya ce jam'iyyar na jiran ganin ko Wike zai gabatar da kansa don a tantance shi.

PDP ta bayyana lokacin da za ta yanke hukunci kan makomar Wike

A wani labarin, jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ta yi martani a kan zabar tsohon gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya yi a matsayin minista.

Mukaddashin shugaban jam'iyyar PDP na kasa, Ambasada Umar Damagum, ya ce jam'iyyar za ta dauki kwakkwaran mataki kan nadin Wike.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng