Lauya Ya Bukaci Majalisar Dattawa Ta Haramtawa Stella Okotete Zama Ministar Tinubu, Ya Fadi Dalili

Lauya Ya Bukaci Majalisar Dattawa Ta Haramtawa Stella Okotete Zama Ministar Tinubu, Ya Fadi Dalili

  • An buƙaci Majalisar Dattawa ta yi watsi da sunan Stella Okotete, ɗaya daga cikin waɗanda Tinubu zai naɗa ministoci
  • Wani lauya mazaunin Abuja, Oladotun Hassan ne ya miƙa wannan buƙata bisa zarginta da ya yi da cin hanci da rashawa
  • Okotete dai ɗaya ce daga cikin mutane 28 da Shugaba Tinubu ya aika da sunayensu Majalisar Dattawa domin a tantancesu

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Abuja - Wani lauya ɗan rajin kare haƙƙin ɗan Adam, Oladotun Hassan, ya rubuta koke ga Majalisar Dattawan Najeriya, inda ya buƙaci majalisar ta haramtawa Stella Okotete zama minista a gwamnatin Tinubu.

Hassan ya ce ya kamata Majalisar Dattawa ta haramtawa Okotete zama minista bisa zargin cin hanci da rashawa da ta yi lokacin da take a bankin Nexim kamar yadda Nigerian Tribune ta wallafa.

Kara karanta wannan

Cutar Mashaƙo Ta Ta Sake Juyowa Kano, Ta Kwantar Da Mutane 130 a Asibiti

Lauya ya buƙaci a wartaki Stella Okotete daga waɗanda Tinubu zai naɗa ministoci
Lauya ya nemi a haramtawa Stella Okotete zama minista a gwamnatin Tinubu. Hoto: Stella Erhuvwuoghene Okotete/ Nigerian Senate
Asali: Facebook

An buƙaci a binciketa kan yadda ta tafiyar da aikinta a banki

Hassan ya bukaci a gudanar da sahihin bincike kan badaƙaloli na maƙudan kuɗaɗe da ya zargi Stella da aikatawa a bankin na Nexim.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya zargeta da amfani da matsyainta wajen damfarar bankin biliyoyin naira da daloli ta hanyar amfani da sunayen wasu kamfanoni na ƙarya.

Hassan ya kuma zargi Okotete da satar kuɗaɗen bankin da sunan bayar da rancen kuɗaɗe ga wasu.

Bai kamata Stella Okotete ta zama minista ba

Har ila yau, lauyan ya nemi Majalisar Dattawa da ta haramtawa Stella zama minista saboda waɗancan dalilan da ya zayyano saboda a cewarsa ba ta cancanci riƙe muƙamin ba.

Ya kuma buƙaci majalisar da ta gudanar da bincike a kanta ba tare da ɓata lokaci ba.

Sannan ya kuma nemi a binciki bayanan karatunta kama daga takardun shaidar kammala karatun da ta bayyana ta samu, zuwa kuɗaɗen makarantar da ta biya a lokacin karatun na ta.

Kara karanta wannan

Aikin Likita, Banki Da Abubuwa 3 Da Ya Kamata Ku Sani Game Da Ministan Jonathan Da Ya Shiga Cikin Ministocin Tinubu

Haka nan ya buƙaci majalisar ta binciki yadda ta gudanar da bautar ƙasarta da kuma kudaɗen alawus da aka riƙa ba ta a lokacin.

Mutane 11 da ake hasashen Tinubu zai aika da sunayensu majalisa

A wani hasashe da Legit.ng ta yi, an bayyana sunayen mutane 11 da ake sa ran Tinubu zai tura majalisa don naɗa su ministoci.

Daga cikin waɗanda ake sa ran ganin sunayensu akwai tsohon gwamnan jihar Kano, kuma jagoran ɗariƙar Kwankwasiyya wato Rabiu Musa Kwankwaso.

Asali: Legit.ng

Authors:
Deen Dabai avatar

Deen Dabai Zaharaddeen Hamisu marubuci kuma ma'aikacin jarida ne da ke da gogewa wajen iya tantance sahihan labarai da na karya. Ya yi digirinsa a jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Baya ga haka, ya shafe sama da shekaru 5 a bangaren aikin watsa labarai wanda hakan ya bashi gogewa ta musamman a aikin jarida. Za a iya tuntubarsa ta adireshinsa na yanar gizo: deen.dabai@corp.legit.ng