Zababbun Ministocin Tinubu: PDP Ta Bayyana Lokacin Da Za Ta Yanke Hukunci Kan Makomar Wike
- Jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ta ce za ta yanke hukunci kan makomar Nyesom Wike bayan Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya nada shi minista
- Mukaddashin shugaban PDP na kasa, Ambasada Umar Damagum, ya ce sun rigada sun fara tuntuba kan lamarin Wike
- Damagum ya bayyana cewa PDP za ta gana a ranar Litinin, 31 ga watan Yuli, domin daukar matsaya kan nada Wike minista
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ta yi martani a kan zabar tsohon gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya yi a matsayin minista.
Mukaddashin shugaban jam'iyyar PDP na kasa, Ambasada Umar Damagum, ya ce jam'iyyar za ta dauki kwakkwaran mataki kan nadin Wike.
Mun fara tattaunawa kan lamarin Wike, PDP
Damagum, wanda ya bayyana hakan a wata hirar waya da jaridar The Nation a ranar Juma'a. 28 ga watan Yuli, ya kara da cewar tuni suka fara tuntuba kan lamarin Wike.
Ganduje Ya Gamu da Cikas, Wasu Kusoshin APC Sun Faɗa Wa Tinubu Wanda Ya Cancanci Zama Shugaban APC Na Gaba
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
"Mun riga mun tuntubi kungiyar gwamnonin PDP kan lamarin kuma kwamitin ayyuka na kasa (NWC) zai yi taro a ranar Litinin don daukar kwakkwaran mataki a kai."
Ya musanta zargin cewa PDP ta yi barci tun bayan sanar da sakamakon babban zaben 2023.
Rahoton ya nakalto yana cewa:
“Babu wata tangarda a jam’iyyar PDP kamar yadda kuka ce, don kawai ba ku ga mun hau kan tituna ba. Ana ci gaba da tattaunawa da manyan masu ruwa da tsaki.
“Daga cikin wadanda muke tuntubarsu akwai shuwagabannin jihohi, kungiyar gwamnonin PDP, tsoffin shugabannin kasa da wasu zababbun dattawan PDP.
“Za kuma mu gana da shugabannin kungiyar matasan PDP a mako mai zuwa. Don haka ba mu zaman banza kamar yadda wasu za su yi tunani.”
Babu wani mu'ujiza da za su yi, malamin addini ya yi hasashe kan ministocin Tinubu
A wani labarin kuma, mun ji cewa Primate Elijah Ayodele, shugaban cocin INRI Evangelical Spiritual, ya bayyana abun da Allah ya nuna masa dangane da wadanda shugaban kasa Bola Tinubu ya zaba domin zama ministocinsa.
A cikin bidiyon da ya wallafa a shafinsa na Twitter a ranar Juma'a, 28 ga watan Yuli, malamin addinin ya ce babu ko daya daga cikin ministocin da zai yi wata mu'ujiza da zaran ya isa ofis kuma cewa kasar na bukatar kara kusantar Allah.
Asali: Legit.ng