Mawaki Zai Yi Tsirara Saboda Peter Obi Ya Yi Nasara a kan Bola Tinubu a Kotun Zabe
- Charles Oputa ya na cikin wadanda su ke goyon bayan Peter Obi, su ka tsaya masa a zaben 2023
- Mawakin mai shekara 73 ya bayyana irin farin cikin da zai yi a duk ranar da LP tayi nasara a kotu
- Jam’iyyar adawar da ‘dan takaranta su na shari’a a kotun zabe, su na neman a tsige Bola Tinubu
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Abuja - Shahararren matashin nan kuma mai gwagwarmaya, Charles Oputa wanda aka fi sani da Charley Boy ya dauki babban alkawari.
Charley Boy da yake magana a shafinsa na Twitter a makon nan, ya ce zai yi tunbur idan Peter Obi ya yi nasara a kotun sauraron karar zabe.
Peter Obi wanda ya yi takara a jam’iyyar LP ya na kalubalantar sakamakon zaben 2023 da Bola Ahmed ya lashe a karkashin APC mai-ci.
Zaben 2023: Shin Da Gaske Kotun Daukaka Kara Ta Sanar Da Peter Obi A Matsayin Wanda Ya Lashe Zabe? Bayanai Sun Fito
Saboda tsabagen farin ciki, idan LP za ta samu nasara a kotun da ke sauraron korafin zaben shugaban kasar, Oputa zai yi yawo tsirara a fili.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Mawakin wanda yana cikin manyan magoya bayan Peter Obi ya ce zai yi zindir ne unguwar shugaban kasa Bola Tinubu a jihar Legas.
Alwashin Charley Boy
"Idan kotun sauraron karar zabe ta sanar da cewa Peter Obi ya yi nasara, tun kafinshari’ar ta kai kotun koli, me za ka yi a ranar?
Ni, zan yi yawo tsirara daga karshen unguwar Bodillon har zuwa Falomo [sic].”"
- Charley Boy
Kowa da irin salon da zai dauka
Mutane su na can su na ba Charley Boy amsa, daga masu cewa ga yadda za su yi murna, zuwa masu sukar matsayar da ya dauka.
Idan ya tashi nuna farin ciki, wani mai suna Holy Ghost ya ce kwanaki uku zai yi tsirara.
Alara ya kawo shawarar cewa Charley Boy ya tara masu tukin babur, su cika Legas a ranar domin ayi farin ciki, a maimakon a fito zindir a titi.
Babu abin da mattobrown zai yi illa azumi da addu’ar farin ciki, amma @EzehNnamdiS ya ce zai ajiye aikinsa ne daga jin labarin.
Juyin mulkin Nijar
Kun ji labarin cewa tun tuni wani malamin addinin musulunci ya ce akwai yiwuwar a ga bayan Mohammed Bazoum a Jamhuriyyar Nijar.
Shugaban ya fara nuna zai juyawa Faransa baya ta hanyar buga kudi dabam da CFA, Aliyu Kaduna ya ce hakan zai zama karshen Bazoum.
Asali: Legit.ng