Rikici Ya Barke a Jam'iyyar NNPP, An Ƙori Shugabanni Na Jihohi 7

Rikici Ya Barke a Jam'iyyar NNPP, An Ƙori Shugabanni Na Jihohi 7

  • Rikicin cikin gida da ya addabi jam'iyyar NNPP mai kayan marmari ya buɗe sabon babi yau Jumu'a 28 ga watan Yuli, 2023
  • Kakakin NNPP na kasa, Dakta Agbo Major ya bayyana cewa NWC ya dakatar da shugabannin jam'iyyar na jihohi 7
  • Ya ce jam'iyyar ta daga wa jihohin Imo da Oyo kafa sakamakon zaben gwamna da zaben kananan hukumomi da ke tafe

FCT Abuja - Rigingimun da suka hana jam'iyyar NNPP mai kayan marmari zaman lafiyasun buɗe sabon shafi yayin da kwamitin ayyuka na ƙasa (NWC) ya ɗauki tsattsauran mataki.

Vanguard ta rahoto cewa NWC na NNPP ta ƙasa ya kori kafatanin shugabannin jam'iyyar na rassan jihohi Bakwai a Najeriya.

Jam'iyyar NNPP ta kori shugabanni.
Rikici Ya Barke a Jam'iyyar NNPP, An Ƙori Shugabanni Na Jihohi 7 Hoto: vanguard
Asali: UGC

Mai magana da yawun NNPP na ƙasa, Dakta Agbo Major ne ya bayyana haka yayin hira da manema labarai ranar Jumu'a a birnin tarayya Abuja.

Kara karanta wannan

Dubu Ta Cika: An Kama Ƙasurgumin Ɗan Bindiga da Yaransa 4 da Suka Addabi Mutane a Jihohin Arewa 2

Ya ce waɗan da matakin korar ya shafa a jihohin 7 sun ƙunshi shugabannin jam'iyya na matakin gundumomi, kananan hukumomi da kuma jiha.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Dakta Agbor ya yi bayanin cewa korar jiga-jigan bai saɓa wa tanadin kundin tsarin mulkin jam'iyyar NNPP 2022 wanda aka yi wa garambawul ba.

Jerin jihohin da NWC ya sallami shugabannin NNPP

Kakakin NNPP ya jero jihohin da wannan mataki ya shafa, wanda suka haɗa da, Katsina, Kaduna, Ribas, Enugu, Ekiti, Neja da kuma jihar Zamfara.

Ya kara da cewa an kafa kwamitin rikon kwarya mai ƙunshe da mutum 5 daga domin tafiyar da harkokin jam’iyyar a jihohin da abin ya shafa.

Agbo Major ya ce baya ga korar shugabanni a jihar Enugu, NNPP ta dakatar da dan takarar gwamnan jihar, Cajetan Eze da ɗan takarar sanata, Enugu ta Arewa, Farfesa Onyeka A. Onyeka.

Kara karanta wannan

Bayan Tsawon Lokaci, An Bayyana Sunan Sabon Shugaban Jam'iyyar APC a Jihar Arewa

NNPP ta bayyana cewa ba ta kori shugabanni na jihohin Oyo da Imo ba, duba da zaben gwamna da za a yi a jihar Imo da na kananan hukumomi a jihar Oyo.

Mubarak Dabai, ɗaya daga cikin shugabannin NNPP a ƙaramar hukumar Ɗanja ta jihar Katsina ya shaida wa Legit.ng cewa har yanzun matakin bai ƙariso gare su ba a hukumance.

A cewarsa, akwai buƙatar garambawul a baki ɗaya NNPP tun daga matakin ƙasa har gunduma idan aka yi la'akari da yar rawar da jam'iyyar ta taka a babban zaɓen 2023.

A kalamansa, Mubarak ya ce:

"Gaskiya ban samu labari ba, amma idan haka ne gyaran ai ba a jihohi 7 kaɗai yake ba, kusan kowace jiha da su kansu shugabanni na ƙasa suna bukatar a masu garambawul."
"Idan ka cire Kano jihar Madugu, babu inda zaka ɗaga ka ce NNPP ta tabuka abun a yaba a babban zaben da ya wuce, abin haushi wasu yan takarar janye wa suka riƙa yi, akwai matsala babba a NNPP."

Kara karanta wannan

Anya Ganduje Zai Kai Labari? Gaskiya Ta Bayyana Kan Wanda Zai Zama Sabon Shugaban APC

Orji Kalu Ya Bayyana Yadda Ya Ki Amincewa da Nadin MinistannTinubu, Ya Fadi Dalil

A wani rahoton kuma Sanata Orji Kalu ya ce shugaban ƙasa Bola Tinubu ya masa tayin zama mamban majalisar zartarwa amma ya ƙi amince wa da tayin.

Ya ce fadar shugaban ƙasa ta tunkare shi da wannan tayin mai gwaɓi jim kaɗan bayan ya janye daga takarar shugaban majalisar dattawa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262