Fitaccen Gwamnan PDP Ya Yi Magana Kan Nada Wike a Matsayin Minista
- Siminalayi Fubara ya zama gwamna PDP na farko da ya taya Nyesom Wike murna kan zabe shi a matsayin minista a karkashin shugaba Bola Tinubu
- Gwamnan Fubara na Ribas ya nuna kwarin guiwa da cancantar magabacinsa, yana mai cewa kokarinsa wajen haɗa kan ƙasa ne ya kai shi ga nasara
- Wike, tsohon gwamnan Ribas kuma jigon PDP na cikin ministoci 28 da Sanata Akpabio ya karanta sunansu a zauren majalisar dattawa ranar Alhamis
Rivers state - Gwamnan jihar Ribas, Siminalayi Fubara, ya taya magabacinsa, Nyesom Wike murnar shiga cikin jerin sunayen ministocin da shugaba Bola Tinubu ya nada.
Wike ya kasance gwamnan jihar Ribas na zango biyu wanda wa’adinsa ya kare a ranar 29 ga watan Mayu a karkashin jam’iyyar PDP kuma Fubara ya gaje shi, wanda shi ne dan takarar da ya fi so.
Gwamna Fubara ya taya Wike murna
Da safiyar Juma’a, 28 ga watan Yuli, Gwamna Fubara, a wani sako da ya wallafa a shafinsa na Twitter, ya taya Wike murna bisa naɗin da shugaban ƙasa ya masa a matsayin minista.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamnan Fubara ya yaba wa magabacinsa bisa tsaya wa tsayin daka kan fafutuka da gwagwarmayar haɗa kan ƙasa.
Fubara ya ce:
"Hakika jajircewarka kan hadin kan kasarmu da ci gaban kasarmu shi ne ya kara zaburar da kai wajen tabbatar da daidaito, adalci da gaskiya."
"Mun yi imanin cewa za ka ci gaba da yin tasiri ta hanyar shiga cikin tawagar manyan shugabanni don sauya tarihin kasarmu domin kyautatawa da inganta rayuwar mutane."
Meyasa Tinubu ya naɗa Wike a matsayin Minista?
Masana harkokin siyasa sun daɗe suna muhawara kan dalilin da ya sa shugaban ƙasa ya sanya Wike a cikin jerin ministocinsa.
Yayin da wasu ke ganin hakan ya kamata domin a saka masa bisa aikin da ya yi don samun nasarar Shugaba Tinubu a jihar Ribas a zaben 2023, wasu kuma sun ce ya sayar da PDP ne kan mukamin minista.
Gwamna Aliyu Ya Aika Sunayen Kwamishinoni Ga Majalisar Dokokin Sokoto
A wani labarin kuma Gwamna Ahmed Aliyu ya tura sunayen kwamishinoni 16 zuwa majalisar dokokin jihar Sakkwato ranar Alhamis.
Sunayen wadanda gwamnan ya naɗa na kunshe ne a cikin wata wasika da ya aike wa shugaban majalisar, Alhaji Tukur Bala.
Asali: Legit.ng