2023: Bayanai Sun Fito Akan Gaskiyar Ayyana Peter Obi Da Kotun Daukaka Kara Ta Yi

2023: Bayanai Sun Fito Akan Gaskiyar Ayyana Peter Obi Da Kotun Daukaka Kara Ta Yi

  • Dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar Labour, Peter Obi ya kasance na uku a zaben da aka gudanar a watan Fabrairu na 2023
  • A ranar 1 ga watan Maris, Hukumar Zabe ta sanar da dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar APC, Bola Tinubu a matsayin wanda ya lashe zabe
  • Tun wancan lokaci Peter Obi ke kalubalantar sakamakon zaben da cewa Tinubu ya gaza samun kashi 25 a babban birnin Tarayya, Abuja

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

FCT, Abuja - An wallafa wani faifan bidiyo da ke nuna cewa kotun daukaka kara ta sanar da dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar Labour, Peter Obi wanda ya lashe zabe.

An wallafa bidiyon ne a ranar 18 ga watan Yuli inda mawallafin ya ke ba da tabbacin cewa kotun ta sanar da Peter Obi a matsayin wanda ya yi nasara, Legit.ng ta tattaro.

Kara karanta wannan

Shugaban Kasa Tinubu Na Ganawar Sirri Da Shugaban Kasar Benin, Patrice Talon

An bayyana gaskiyar cewa kotu ta ayyana Peter Obi a matsayin wanda ya lashe zabe
Peter Obi Ya Shigar Da Kara Kotu Kan Magudin Zabe Da Aka Tafka A Watan Faburairu. Hoto: Peter Obi.
Asali: Facebook

Yadda aka yada sanarwar kotun akan zaben Peter Obi

A bayanin, an ce kotun ta tabbatar da haka ne bayan dan takarar ya samu kashi 25 a babban birnin Tarayya, Abuja.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Wanda ya wallafa labarin ya nuna alamun samun wanna bayanin daga gidan talabijin na Arise.

Bidiyon da aka wallafa ya samu fiye da mutane miliyan daya da suka kalla yayin da aka yi ta yada shi.

Binciken kwakwaf ya karyata labarin

Africa Check ta yi binciken kwakwaf inda ta tabbatar cewa labarin kanzon kurege ne don babu sahijiyar gidan jaridar da ta dauki labarin.

Tun bayan sanar da Shugaba Bola Ahmed Tinubu a matsayin wanda ya lashe zabe, jam'iyyun adawa musamman PDP da Labour suka garzaya kotu.

Peter Obi da dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar suna kotu har bayan rantsar da shugaban kasa, Bola Tinubu a watan Mayu.

Kara karanta wannan

"Tsohon Shugaban Majalisa Ya Jawowa Abdullahi Adamu Rasa Shugabacin APC"

"Har Yanzu Peter Obi Yana Da Sauran Dama": Faston Da Ya Hango Nasarar Tinubu A Baya Ya Yi Martani

A wani labarin, wani shahararren Fasto mai suna Godwin Ikuru ya shawarci dan takarar shugaban kasa a jam'iyar Labour, Peter Obi ya janye karar da ya shigar akan zabe.

Ikuru wanda ya taba hasashen shugaban kasa Tinubu zai yi mulkin kasar, ya ce ya hango Peter Obi ba shi da wata sauran nasara a kotun sauraran kararrakin zaben.

Faston ya bayyana haka ne yayin hira da manema labarai a ranar Talata 18 ga watan Yuli.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.