Barista Idris Shuaibu Ya Zama Sabon Shugaban APC Reshen Jihar Adamawa

Barista Idris Shuaibu Ya Zama Sabon Shugaban APC Reshen Jihar Adamawa

  • Barista Idris Shu'aibu ya samu nasarar zama sabon shugaban APC ta jihar Adamawa bayan taron kwamitin SEC
  • Tsohon shugaban, Ibrahim Bilal ya rasa muƙaminsa ne kan zargin karkatar da kuɗaɗen jam'iyya a 2022
  • APC na fama da rikicin cikin gida a jihar Adamawa tun bayan kammala zaben fidda gwani na takarar gwamna

Adamawa state - A ranar Alhamis, 27 ga watan Yuli, 2023 ne aka nada Barista Idris Shuaibu a matsayin sabon shugaban jam’iyyar APC reshen jihar Adamawa.

Kafin zaɓen sabon shugaban, Ismaila Tadawus ne ke jagorantar APC ta Adamawa a matsayin muƙaddashin shugaba bayan tunbuke Ibrahim Bilal daga kujarar shugaban jam'iyya.

An zabi sabon shugaban APC a Adamawa.
Barista Idris Shuaibu Ya Zama Sabon Shugaban APC Reshen Jihar Adamawa Hoto: dailytrust
Asali: Twitter

Jaridar Daily Trust ta tattaro cewa an tsige Bilal daga matsayin shugaban APC na jihar a shekarar 2022 bisa zargin almubazzaranci da kuɗaɗen jam'iyya.

Kara karanta wannan

Bayan Janye Masa Takara, Mace Ɗaya Tilo Da Ta Nemi Tikitin APC Ta Samu Babban Mulki a Gwamnatin Tinubu

Kwamitin zartarwa na jiha (SEC) ne ya amince da naɗin Barista Shu'aibu a matsayin shugaban APC a wani taron gaggawa da ya gudana a Yola, babban birnin Adamawa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Da yake jawabi a wajen taron, sakataren jam’iyyar APC na jihar, Dakta Raymond Chidama, ya ce kwamitin ya yi aiki ne da wata takarda daga mazaɓar Sanatan Adamawa ta arewa.

Takardar ta ayyana goyon baya ga Shuaibu bisa la’akari da halayensa na jagoranci da kuma yadda ya gudanar da ayyukansa a matsayinsa na mai bai wa APC shawara kan harkokin shari’a.

Zamu haɗa kan mambobi wuri ɗaya - Barista Shu'aibu

A jawabinsa, sabon shugaban ya ce gwamnatinsa za ta ba da fifiko wajen sulhuntawa tsakanin ɓangarorin jam’iyyar daban-daban, inda ya nemi goyon baya daga masu ruwa da tsaki.

Jam'iyyar APC a Adamawa ta shiga rudani sakamakon rashin jituwar da ta kunno kai a zaben fidda gwani na ɗan takarar gwamna a zaben 2023 da ya gabata, Daily Post ta rahoto.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Sanatan APC Na Shirin Murabus Daga Majalisar Dattawa, Sahihan Bayanai Sun Fito

Tsagi ɗaya na biyayya ga Sanata Aishatu Binani, ‘yar takarar gwamna a inuwar APC a zaben da ya gabata, ɗayan kuma Nuhu Ribadu, mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro.

Shugaban Kasa Tinubu Ya Yi Sabbin Naɗe-Naɗe a Hukumar NCS

A wani rahoton kuma Shugaban ƙasa Bola Tinubu ya yi sabbin naɗi guda 6 a hukumar kwastam ta ƙasa (NCS).

Tinubu ya naɗa mataimakan kwanturola janar na hukumar kwastam guda 3 da kananan mataimaka guda 3.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262