Ganduje da Tsofaffin Gwamnoni 7 da Tinubu Ya Watsar Wajen Rabon Mukaman Minista
- A ranar Alhamis Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya aikawa majalisar dattawa sunayen wasu Ministoci
- Sahun farko na wadanda ake so su zama Ministoci a gwamnatin tarayya sun hada da Malam Nasir El Rufai
- Jerin ya kunshi Sani Abubakar Danladi, amma ba a ga sunayen wasu tsofaffin Gwamnoni na APC ba
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Abuja - Duk da jerin na farko yana dauke da tsofaffin gwamnoni kamar Nasir El Rufai, Badaru Abubakar da Nyesom Wike, wasu ba su yi dace ba.
Rahoton nan ya tattaro maku tsofaffin Gwamnonin APC ko akalla su ka taimakawa jam’iyya mai-mulki a zaben 2023, da ba su samu kujerar ba tukun.
1. Abdullahi Umar Ganduje
Babu sunan Abdullahi Umar Ganduje wanda ya yi shekaru takwas yana mulki a jihar Kano, ana kyautata zaton zai iya zama sabon shugaban APC na kasa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
2. Gboyega Oyetola
An yi tunanin Gboyega Oyetola zai samu mukami zuwa yanzu saboda kusancinsa da shugaban kasa da kuma ganin ya rasa kujerar Gwamnan Osun a 2022.
3. Atiku Bagudu
Zuwa yanzu Sanata Atiku Bagudu bai cikin wadanda su ka samu mukaman Minista duk da tsohon Gwamnan ya rike kungiyar gwamnonin jihohin APC.
4. Ben Ayade
Baya ga cewa bai lashe zaben Sanata a 2023 ba, Farfesa Beyn Ayade bai samu shiga cikin jerin Ministoci ba, amma an aika sunan Kwamishinarsa, Ben Edu.
5. Simon Lalong
Ganin shi ya rike shugabancin kwamitin yakin neman zaben Bola Tinubu, kowa ya yi tunani Simon Lalong zai samu mukami, a yanzu dai ba haka aka yi ba.
6. Bello Matawalle
Duk da Bola Tinubu ya yi nasara a Zamfara, Bello Matawalle bai zarce a matsayin Gwamna a APC ba, wasu sun yi tunanin zai rage zafi da kujera a FEC.
7. Akinwumi Ambode
Akinwumi Ambode ya rasa tikitin APC da kujerar Gwamnan Legas ne tun 2019, amma bai fice daga jam’iyyar ba, watakila ya wakilci Legas a jeri na biyu.
Musawa, Stella Okoteteda da Ohaneye.
An ji labari Bola Tinubu ya dauko mai digiri 6, da wata mai shekara 36 da kuma matar da kammala digiri ta na shekara 19, zai nada a matsayin Ministoci.
A matan akwai tsohuwar kwamishinar Imo, Dr. Diris Anite Uzoka, Betta Edu wanda ita ce shugabar mata a APC, da tsohuwar ‘yar majalisa Nkiru Onyejiocha.
Asali: Legit.ng