Bello El-Rufai Da 'Yar James Ibori Sun Samu Manyan Kwamitoci a Majalisar Wakilai
- A ranar Alhamis ne aka yi rabon kwamitoci a Majalisar Wakilan Najeriya ta 10
- Kakakin Majalisar Wakilan Najeriya, Tajuddeen Abbas ne ya raba kwamitocin ga 'yan majalisun
- Wasu Daga Cikin 'yan majalisun sun yi sa'ar dawowa kan kwamitocin da suka taɓa riƙewa a baya
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Abuja - An bayyana sunayen kwamitocin da aka bai wa ɗan El-Rufai wato Bello El-Rufai da kuma ɗiyar James Ibori, tsohon gwamnan jihar Delta, Erhiatake Ibori-Suenu.
Kakakin Majalisar Wakilai, Tajuddeen Abbas ne ya bayyana kwamitocin a zaman majalisar na ranar Alhamis, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.
Muƙaman da aka bai wa Bello El-Rufai da Ibori-Suenu
An bai wa ɗiyar Ibori shugabar kwamitin majalisa kan harkokin hukumar raya yankin Neja Delta (NDDC), a yayin da aka bai wa ɗan El-Rufai shugabancin kwamitin majalisar kan harkokin bankuna.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Tsohon mataimakin kakakin majalisar, Ahmed Idris Wase, tsohon shugaban masu rinjaye na Majalisar Wakilai Alhassan Doguwa, Yusuf Adamu Gagdi da Mukhtar Betara suma sun samu shugabancin kwamitoci masu gwaɓi.
Ikenga Ugochinyere ya zama shugaban kwamitin albarkatun man fetur (ɓangaren sarrafawa), yayin da Alhassan Ado Doguwa ya zama shugaban kwamitin albarkatun man fetur (ɓangaren haƙo mai).
Ƙarin kwamitocin da aka bai wa wasu 'yan majalisun shugabancinsu
Kabir Alhassan Rurum, ya samu shugabancin kwamitin harkokin sufurin jiragen sama na majalisa, yayin da Abdulmumini Jibrin Kofa ya samu shugabancin kwamitin majalisar kan harkokin ƙasashen waje.
Abubakar Kabir Abubakar Bichi, wanda shi ne tsohon shugaban kwamitin ayyuka a majalisa ta tara, yanzu shi ne ya zama shugaban kwamitin kasafin kudi.
Betara wanda ya riƙe shugabancin kwamitin kasafin kudi a majalisa ta tara, a yanzu shi ne zai shugabanci kwamitin majalisar kan harkokin babban birnin tarayya.
El-Rufai Na Iya Zama Ministan Wutar Lantarki Yayin da Jerin Sunayen Ministoci Ya Isa Gaban Majalisar Dattawa
Yusuf Adamu Gagdi zai ci gaba da riƙe shugabancin kwamitin majalisar kan sojojin ruwa kamar yadda ya zo a rahoton Daily Trust.
Jihohi 11 da ba a bayyana sunayen waɗanda za a ba ministoci ba
Legit.ng a baya ta kawo rahoto dangane da batun jerin sunayen mutane 28 da Shugaba Tinubu ya aika Majalisar Dattawa don a tantancesu.
Sai dai an gano cewa akwai jihohi aƙalla 11 da ba a sunan koda mutum ɗaya nasu a cikin jerin sunayen.
Asali: Legit.ng