Jerin Jihohin Da Basu Samu Kujerun Ministoci Ba Zuwa Yanzu a Gwamnatin Shugaban Kasa Tinubu

Jerin Jihohin Da Basu Samu Kujerun Ministoci Ba Zuwa Yanzu a Gwamnatin Shugaban Kasa Tinubu

Shugaban kasa Bola Tinubu ya mika sunayen ministoci 28 zuwa majalisar dattawa a ranar Alhamis, 27 ga watan Yuli domin tantance su.

Bayan an dangata gaba daya sunayen da ya mika majalisa da jihohinsu na asali, an gano cewa wasu jihohi 11 basu samu kujerun ministoci ba tukuna.

Shugaban kasa Bola Tinubu
Jerin Jihohin Da Basu Samu Kujerun Ministoci Ba Zuwa Yanzu a Gwamnatin Shugaban Kasa Tinubu Hoto: @officialABAT
Asali: Twitter

Kamar yadda sashi na 147(3) na kundin tsarin mulkin 1999 ya tanadar, dole shugaban kasa ya zabi akalla minista daya daga kowace jiha, wanda zai zama dan asalin wannan jiha, jaridar The Cable ta rahoto.

Bisa ga nazarin da aka yi kan sunayen da shugaban kasar ya aika majalisa, Katsina, Cross River, da Bauchi suna da ministoci bibbiyu, yayin da wasu jihohi 11 basu da ko daya zuwa yanzu.

Ga jerin jihohin da basu samar da ministoci ba zuwa yanzu a kasa:

Kara karanta wannan

Sunayen Ministoci: Gbajabiamila Ya Fadi Lokacin Da Tinubu Zai Bayyana Na Kano, Legas Da Sauran Jihohin

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

  1. Adamawa
  2. Bayelsa
  3. Gombe
  4. Kano
  5. Kebbi
  6. Kogi
  7. Lagas
  8. Nasarawa
  9. Osun
  10. Yobe
  11. Zamfara

Majalisa ta karanto sunayen mutane 28 da Tinubu ya gabatar a matsayin ministoci

A baya Legit.ng ta rahoto cewa Shugaban Majalisar Dattawa Godswill Akpabio ya iso zauren majalisar tarayya kuma an fara zaman majalisa yayin da yan Najeriya ke jiran jerin sunayen ministocin Shugaba Bola Ahmed Tinubu.

Sabuwar doka da aka yi a Najeriya ta ba wa shugaban kasa kwana 60 ya fitar da ministocinsa kuma wannan wa'adin zai cika zuwa karshen wannan makon.

Sanata Godswill Akpabio ya karanto jerin sunayen da aka aiko masa, yana farawa da Abubakar Momoh da Yusuf Tuggar CON.

Wasikar da Bola Tinubu ya rubuto ba ta kunshi Jihohin da aka zakulo Ministocin ba.

Jerin tsoffin gwamnoni da suka samu shiga cikin ministocin Tinubu

Kara karanta wannan

Jerin Asalin Jihohin Ministoci 28 Da Shugaba Bola Tinubu Ya Naɗa

A wani labarin kuma, mun ji cewa daga cikin wadanda aka zaba akwai wasu tsoffin gwamnoni wadanda za su yi aiki a matsayin ministoci a karkashin gwamnatin shugaban kasa Tinubu.

Ya zama kamar wata al'ada shugabannin kasa su zabi tsoffin gwamnoni a matsayin ministoci idan suka kammala wa'adin mulkinsu.

Nasir El-Rufai

Mallam El-Rufai ya kasance tsohon gwamnan jihar Kaduna,wanda ya jagoranci jihar har sau biyu, kuma sunansa na daga cikin sabbin ministocin da za su yi aiki tare da Shugaban kasa Tinubu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng