"Zasu Iya Aiki a Ko Ina" Gbaja Ya Yi Bayanin Kan Ma'aikatun Ministocin Tinubu

"Zasu Iya Aiki a Ko Ina" Gbaja Ya Yi Bayanin Kan Ma'aikatun Ministocin Tinubu

  • Fadar shugaban ƙasa ta bayyana dalilin da ya sanya shugaba Tinubu bai raba wa ministocinsa ma'aikatun da zasu riƙe ba
  • Femi Gbajabiamila ya ce raba ma'aitun tun da fari zai taimaka wa majalisa wajen tantance wa, amma Tinubu ya san dukka zasu iya aiki a ko ina
  • Gbaja ya ce yayin da majalisa ke aikin tantancewa, Tinubu da tawagarsa zasu maida hankali wajen nazari kan inda za a tura su

Abuja - Femi Gbajabiamila, shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasa, ya bayyana dalilin da ya sa Bola Tinubu bai raba wa ministocin da ya naɗa ma'aikatun da zasu yi aiki ba.

Jaridar The Cable ta ruwaito cewa a ranar Alhamis ne Tinubu ya aika sunayen ministoci 28 zuwa majalisar dattawa domin tantancewa tare da amince wa da su.

Kara karanta wannan

Fadar Shugaban Kasa Ta Fayyace Adadin Ragowar Ministocin da Za a Nada

Femi Gbajabiamila da shugaba Tinubu.
"Zasu Iya Aiki a Ko Ina" Gbaja Ya Yi Bayanin Kan Ma'aikatun Ministocin Tinubu Hoto: Femi Gabajabiamila
Asali: Twitter

Da yake hira da manema labarai bayan gabatar da sunayen, Gbaja ya ce yayin da za a ci gaba da gudanar da aikin tantancewar, Tinubu da tawagarsa za su samu damar tantance wurin da ya fi dacewa da kowane minista.

Meyasa Tinubu bai bayyana ma'aikatun da ministocin zaau ja ragama ba?

Leadership ta tattaro shi yana cewa:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Ina son ra'ayin haɗa kowane suna da ma'aikatar da zai jagoranta, saboda haka zai ba majalisar dattawa damar ta san ainihin abin da zata tambayi kowane mutum ɗaya a kansa."
"Amma a yanzu, muna tunanin cewa yana da kyau mu tsaya kan al'adar aika sunayen sannan kuma yayin da ake gudanar da aikin tantancewa, mu ba shugaba da tawagarsa damar duba kundin bayanai kowa su ga inda ya dace "
"Abu na farko da ya duba shi ne wadannan mutane ne da za su iya aiki a duk inda ka sanya su, sai dai wasu fannoni na musamman kamar Antoni Janar. Amma (Tinubu) ya yi imanin mafi yawansu za su iya shiga ko'ina."

Kara karanta wannan

Kace-Nace Yayin Da 'Yan Najeriya Suka Soki Yadda Tinubu Ya Zabi Ministoci, Sun Bayyana Abin Da Ya Kamata

Gbajabiamila ya kara da cewa abu mafi muhimmanci, shugaba Tinubu na da niyyar raba wasu ma'aikatun kuma da ywuwar ya ƙirƙiri sabbin ma'aikatu.

Bayan Janye Masa, Yar Takara Mace Ɗaya Tilo Ta Shiga Cikin Ministocin Tinubu

A wani rahoton na daban Honorabul Uju Kennedy Ohaneye, mace ɗaya tilo da ta nemi tikitin shugaban ƙasa a inuwar APC ta shiga jerin ministocin shugaba Tinubu.

A ranar Alhamis, 27 ga watan Yuli, shugaba Tinubu ya aika sunayen ministocin da aka jima ana dako ga majalisar tarayya domin tantancewa

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262