Shugaba Tinubu, Shugaban Matasa Na APC Na Taron Gaggawa
- A ranar Alhamis, 27 ga watan Yuli, Tinubu ya karɓi baƙuncin shugabannin matasan jam'iyyar APC
- Taron dai na zuwa ne jim kaɗan bayan da Tinubu ya aikawa Majalisar Dattawa sunayen mutane 28 da zai naɗa ministoci
- Tinubu ya bayyana cewa matasan Najeriya na daga cikin 'yan gwagwarmayar siyasar yanzu, kuma su ne za su ci gaba da tafiyar da ƙasar a gaba
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Abuja - Rahotanni sun nuna cewa shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu, ya shiga wata ganawa ta sirri da shugabannin matasan jam'iyyar APC a fadar Gwamnatin Tarayyar Najeriya da ke Abuja.
Gidan talabijin na NTA ne ya bayyana rahoton taron, wanda ya samu halartar da dama daga shugabannin matasan na jam'iyyar ta APC.
Abinda Tinubu ya faɗawa shugabannin matasan na APC
Bayan Janye Masa Takara, Mace Ɗaya Tilo Da Ta Nemi Tikitin APC Ta Samu Babban Mulki a Gwamnatin Tinubu
Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da Tinubu ya aika da sunayen mutane 28 daga cikin waɗanda yake so ya bai wa muƙaman ministoci.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Tinubu a lokacin da yake ganawa da shugabannin matasan jam'iyyar ta APC, ya bayyana musu cewa suna daga cikin masu tafiyar da gwamnati a yanzu, kuma su ne za su ci gaba da tafiyar da ƙasa a gaba.
Matasan APC sun nemi Tinubu ya tuna da su wajen rabon muƙamai
Shugabannin matasan jam'iyyar APC sun yi kira ga Shugaba Tinubu da ya sanya su cikin ministocinsa.
Sai dai abinda ya bayyana a sunaye 28 da Shugaban Tinubu ya tura a tantancesu don naɗa su ministoci ya nuna babu lissafin matasa a ciki.
Sai dai da alamu ba a mance da mata ba tunda an ga sunan Uju Kennedy Ohaneye, wacce ita ce mace ɗaya tilo 'yar takarar shugabancin ƙasa a APC da ta janyewa Tinubu.
Sanatan APC zai yi murabus daga kan kujerarsa
Legit.ng a baya ta yi rahoton kan tsohon gwamnan jihar Ebonyi kuma sanata mai ci a jam'iyyar APC David Umahi, da zai yi murabus daga kujerarsa ta sanata.
Hakan ya biyo bayan bayyana sunansa da aka yi cikin sabbin ministocin da Shugaba Tinubu zai naɗa.
A ranar 27 ga watan Yuli ne dai Shugaba Tinubu ya aikawa Majalisar Dattawan Najeriya sunayen mutane 28 da yake so ya yi aiki da su a matsayin ministoci a gwamnatinsa.
Asali: Legit.ng