Abubuwa 5 Da Ya Kamata Ku Sani Game Da Ministan Jonathan Mohammed Pate Wanda Ya Shiga Jerin Ministocin Tinubu

Abubuwa 5 Da Ya Kamata Ku Sani Game Da Ministan Jonathan Mohammed Pate Wanda Ya Shiga Jerin Ministocin Tinubu

Farfesa Mohammed Ali Pate wanda ɗan jihar Bauchi ne, ya samu damar shiga cikin jerin ministocin da Shugaba Tinubu zai naɗa cikin 'yan kwanakin nan.

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Godswill Akpabio ne ya karanto sunayen mutane 28 da shugaban ƙasa ya aikawa majalisar domin a tantancesu.

Mohammed Ali Pate ya shiga jerin ministocin Tinubu
Abubuwa 5 da ya kamata ku sani kan Mohammed Pate, tsohon minista a lokacin Jonathan. Hoto: @mohammedpate
Asali: Twitter

Abubuwa 5 dangane da Mohammed Ali Pate

Kamar yadda jaridar Vanguard ta ruwaito, waɗannan wasu abubuwa ne guda 5 da ya kamata ku sani game da sabon ministan Tinubu, Farfesa Mohammed Ali Pate:

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Tsohon minista a lokacin Jonathan

Mohammed Pate ya riƙe muƙamin ƙaramin ministan lafiya a lokacin tsohon shugaban ƙasa Goodluck Ebele Jonathan.

Ya riƙe muƙamin ne na tsawon shekaru 2, daga shekarar 2011 zuwa shekarar 2013, inda ya ajiye muƙamin ministan domin karɓar wani muƙamin a ƙasar Amurka.

Kara karanta wannan

‘Ba Batun Neman Minista Ba Ne’, Jonathan Ya Bayyana Dalilin Kai Wa Tinubu Ziyara

Ya yi karatu a jami'ar ABU Zaria

Mohammed Pate ya kammala digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria ta jihar Kaduna.

Pate ya karanci ɓangaren likitanci a jami'ar ABU, inda ya kammala a shekarar 1990.

Aiki a fannin lafiya

Ali Pate ya kasance ƙwararren likita a ɓangaren cututtuka masu yaɗuwa.

Ya yi digirinsa na biyu a fannin kula da lafiya a makarantar tsafta da kiwon lafiya da ke birnin Landan ta ƙasar Ingila.

Haka nan ya yi wani digirin a bangaren kula da kasuwanci a jami'ar Duke da ke Arewacin birnin Carolina na ƙasar Amurka.

Aiki da bankin duniya

Ali Pate ya kasance tsohon daraktan kula da kiwon lafiya, abinci da yawan jama'a na bankin duniya.

Haka nan Pate ya kuma taɓa riƙe muƙamin wata ƙungiya da ke tallafawa mata, matasa da ƙananan yara wato GFF.

Kin karɓar shugabancin GAVI

A kwanakin baya ne Muhammad Ali Pate ya ƙi karɓar wani tayi da aka yi masa na shugabantar wata ma'aikatar lafiya ta duniya mai suna GAVI kamar yadda Leadership ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Gwamnatin Jihar Bauchi Ta Kulle Makarantu Saboda Bullar Cutar Mashako, Ta Bayyana Matakin Dauka Na Gaba

GAVI wata ma'aikata ce da ke ba da agajin rigakafin cututtuka a ƙasashen da ke da raunin tattalin arziƙi.

Mata 7 da suka samu shiga cikin jerin ministocin Tinubu

Legit.ng a baya ta kawo muku rahoto kan mata bakwai da sunayensu ya fito cikin jerin ministocin da Tinubu zai naɗa.

An bayyana cewa matan da Hannatu Musawa, Betta Edu, Stella Okotette, Doris Uzoka-Anite, Nkeiruka Onyejeocha, Uku Kennedy-Ohaneye da kuma Iman Suleiman.

Asali: Legit.ng

Authors:
Deen Dabai avatar

Deen Dabai Zaharaddeen Hamisu marubuci kuma ma'aikacin jarida ne da ke da gogewa wajen iya tantance sahihan labarai da na karya. Ya yi digirinsa a jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Baya ga haka, ya shafe sama da shekaru 5 a bangaren aikin watsa labarai wanda hakan ya bashi gogewa ta musamman a aikin jarida. Za a iya tuntubarsa ta adireshinsa na yanar gizo: deen.dabai@corp.legit.ng