Shehu Sani Ya Yi Martani Kan Sunayen Ministocin Shugaba Tinubu
- Majalisar dattawa ta sanar da jerin sunayen ministocin Shugaba Bola Tinubu da aka daɗe ana zaman jira
- Sanata Shehu Sani ya bayyana cewa Shugaba Tinubu ya zaɓi wasu baragurbi daga cikin ministocin nasa
- Shugaban majalisar dattawa, Sanata Godswill Akpabio ya sanar da sunayen mutum 28 da aka zaɓo domin zama ministoci a zaman majalisar na ranar Alhamis
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Tsohon Sanatan Kaduna ta Tsakiya, Sanata Shehu Sani, ya yi martani kan jerin sunayen ministocin Shugaba Bola Tinubu, da shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio ya karanto.
Sani ya bayyana cewa Shugaba Tinubu ya zaɓo wasu macizai waɗanda sanannu ne wajen cin amana sannan ya sakawa wasu macizai waɗanda sanannu ne wajen cin amana.
Tsohon sanatan ya kuma yi gargaɗin cewa, ƙoƙarin faranta ran maciji ba zai sa Sarki ya tsira ba.
Shehu ya bayyana hakan ne a wani rubutu da ya yi a shafinsa na Twitter @ShehuSani a ranar Alhamis, 27 ga watan Yuli.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
A kalamansa:
"Jerin Ministoci; Shugaban ƙasa ya rungumi wasu macizai waɗanda tarihi ya nuna mashahuran mayaudara ne, kuma ya saka wa wasu ƴan a ɓata ruwa domin kowa ya rasa."
"Lallashin maciji a fada ba ya hana ya sari sarki ."
Ko da su wa Shehu Sani yake nufi da kalaman nasa?
Duk da dai tsohon sanatan bai fito fili ya ambaci waɗanda ya yi wannan kalaman domin su ba, ana ganin cewa kalaman nasa ya yi su ne bayan ya hango sunan tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir Ahmad El-Rufai a cikin jerin sunayen ministocin.
Shehu Sani da El-Rufai sun daɗe basa ga maciji bayan sun samu saɓanin siyasa a tsakaninsu.
Tun kafin Shugaba Tinubu ya bayyana sunayen ministocinsa, sai da Shehu Sani ya yi kira da shugaban ƙasar ya yi taka tsantsan wajen ba El-Rufai muƙami, domin a cewarsa tsohon gwamnan mage ce mai kwanciyar ɗaukar rai.
Shugaba Ya Aike Da Sunayen Ministoci Gaban Majalisa
Da zu rahoto ya zo cewa jerin sunayen ministocin Shugaba Tinubu ya isa gaban majalisar dattawan Najeriya.
Shugaban majalisar dattawa Sanata Godswill Akpabio ya karanto sunayen ministocin su 28 waɗanda a ciki har da tsaffin gwamnoni.
Asali: Legit.ng