Wike, El-Rufai Da Wasu Tsoffin Gwanoni 4 Da Suka Shiga Jerin Ministocin Tinubu

Wike, El-Rufai Da Wasu Tsoffin Gwanoni 4 Da Suka Shiga Jerin Ministocin Tinubu

Shugaban kasa Bola Tinubu ya mika sunayen ministocinsa gaban majalisar dokokin tarayya a safiyar Alhamis, 27 ga watan Yuli.

Daga cikin wadanda aka zaba akwai wasu tsoffin gwamnoni wadanda za su yi aiki a matsayin ministoci a karkashin gwamnatin shugaban kasa Tinubu.

Tsoffin gwamnoni da suka zama ministoci
Wike, El-Rufai Da Wasu Tsoffin Gwanoni 4 Da Suka Shiga Jerin Ministocin Tinubu Hoto: Nyesom Wike, Nasir El-Rufai
Asali: Twitter

Ya zama kamar wata al'ada shugabannin kasa su zabi tsoffin gwamnoni a matsayin ministoci idan suka kammala wa'adin mulkinsu.

Ga jerin tsoffin ministoci da suka samu shiga jerin ministocin Tinubu a kasa:

Nasir El-Rufai

El-Rufai ya kasance gwamnan jihar Kaduna sau biyu, kuma sunansa na cikin sabbin ministocin da za su yi aiki tare da Shugaban kasa Tinubu.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Tsohon gwamnan na jihar Kaduna ya taba rike mukamin ministan babban birnin tarayya Abuja a karkashin mulkin tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo.

Kara karanta wannan

Jerin Jihohin Da Basu Samu Kujerun Ministoci Ba Zuwa Yanzu a Gwamnatin Shugaba Tinubu

Nyesom Wike

Tsohon gwamnan jihar Ribas ma ya samu shiga cikin jerin ministocin da shugaban kasa Tinubu ya gabatar da sunayensu a majalisar dattawa domin tantance su.

Koda dai ya kasance jigon Peoples Democratic Party (PDP) ne, an tattaro cewa Wike ya marawa Tinubu na jam'iyyar All Progressives Congress (APC) baya a zaben shugaban kasa na 2023.

David Umahi

Tsohon gwamnan jihar Ebonyi ya kasance cikin jerin zababbun ministocin da shugaban kasa Tinubu ya tura sunayensu majalisar dattawa a ranar Alhamis.

Umahi ya sakance sanata a yanzu haka kuma ana sa ran zai yi murabus daga kujerarsa yayin da za a gudanar da zaben cike gurbi a yankinsa.

Abubakar Badaru

Badaru shine tsohon gwamnan jihar Jigawa, wanda ya yi mulki tsakanin 2015 zuwa 2023.

Yana daya daga cikin amintattun Shugaban kasa Tinubu wadanda shugaban majalisar dattawa Akpabio ya karansu cikin ministoci a ranar Alhamis.

Gboyega Oyetola

Kara karanta wannan

Majiyoyi Sun Bayyana Wanda Tinubu Zai Iya Nadawa a Matsayin Ministan Lafiya Yayin da Ya Mika Sunayensu Majalisa

Oyetola ya kasance gwamnan jihar Osun sau daya kuma an tattaro cewa yana daga cikin wadanda shugaban kasa Tinubu ke so su yi masa aiki a matsayin minista koda dai babu sunansa a cikin wadanda aka karanto a majalisa a ranar Alhamis amma jaridar Punch ta rahoto cewa yana cikin jerin sunayen da za a fitar a karshe.

Dan siyasar na Osun bai samu damar komawa kujerarsa a matsayin gwamnan jihar ba saboda ya sha kaye a hannun Ademola Adeleke na PDP a zaben gwamna na Yulin 2023.

Ben Ayade

Ayade yana cikin tsoffin gwamnonin da suka kammala wa'adinsu na biyu kwanan nan a jihar Cross River karkashin inuwar APC, ba a riga an sanar da sunansa ba kasancewar baya cikin rukunin farko da aka mika sunayensu majalisar dattawa.

Tsohon gwamnan ya sha kaye a kokarinsa na zama sanata inda dan takarar PDP ya yi nasara a zaben ranar 25 ga watan Fabrairu.

Kara karanta wannan

Jihohi 16 Da Ake Dakon Sunayen Kwamishinoni Ana Saura Kwana 1 Wa’adi Ya Kare, Babu Dalili

Jerin jihohi 11 da basu samu kujerun ministoci ba tukuna

A gefe guda, mun ji cewa shugaban kasa Bola Tinubu ya mika sunayen ministoci 28 zuwa majalisar dattawa a ranar Alhamis, 27 ga watan Yuli domin tantance su.

Daga jerin sunayen da ya gabatarwa majalisa, har yanzu wasu jihohin basu samu kujerun ministoci ba bisa la'akari da aka yi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng