Wike, Oyetola Da Sauran Sunayen Da Ke Cikin Ministocin Shugaba Tinubu
- Bayan dogon jira kan sunayen waɗanda Shugaba Tinubu zai naɗa ministoci, Shugaban ƙasan ya aike da sunayen ga majalisar dattawa
- Shugaba Tinubu ya dauƙo tsaffin gwamnoni da wasu daga cikin na kusa da shi domin zama ministoci a gwamnatinsa
- El-Rufai, Wike, Badaru da Ayade na daga cikin jerin ministocin waɗanda majalisa za ta tantance a sati mai zuwa
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
FCT, Abuja - Tsohon gwamnan jihar Rivers, Nyesom Wike da takwaransa na jihar Kaduna, Nasir El-Rufai na daga cikin jerin sunayen ministocin Shugaba Tinubu da aka aikewa majalisar dattawa da su yau da safe.
Jaridar The Nation ta rahoto cewa yau da safe aka aike da jerin sunayen ga shugaban majalisar dattawa, Sanata Godswill Akpabio.
Sauran waɗanda aka zaɓa domin ba muƙamin ministoci sun haɗa da Lateef Fagbemi (SAN), Ali Pate, Olawale Edun, Adebayo Adelabu, da tsohon gwamnan jihar Osun, Adegboyega Oyetola.
Sauran sun haɗa da shugabar mata ta jam'iyyar All Progressives Congress (APC) Mrs. Betta Edu, Sanata Ben Ayade da Dele Alake, wanda ke riƙe da muƙamin babban mai ba da shawara kan sadarwa, tsare-tsare da ayyuka na musamman ga Shugaba Tinubu.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
TheCable ta rahoto cewa David Umahi, tsohon gwamnan jihar Ebonyi, Atiku Bagudu, tsohon gwamnan jihar Kebbi, Mohammed Badaru, tsohon gwamnan jihar Jigawa, Tokunbo Abiru da David Edevbie na daga cikin jerin sunayen ministocin da aka tura zuwa ga majalisar dattawa.
Dalilin aikewa da sunayen ministocin kafin ranar Juma'a
Shugaban ƙasar ya aike da sunayen ministocin ƙafin nan da ranar Juma'a saboda bin umarnin sashi na 42(a) na kundin tsarin mulki, wanda ya umarci dole duk wanda za a zaɓa minista sunan shi ya bayyana a gaban majalisa a cikin kwana 60 da hawan shugaban ƙasa kan mulki.
Wannan wa'adin na kwana 60 yana cika ne a ranar Juma'a, 28 ga watan Yuli, domin an rantsar da Shugaba Tinubu kan kujerar mulki a ranar 29 ga watan Mayun 2023.
A cewar wata majiya, majalisar dattawan za ta tantance ministocin ne a sati mai zuwa.
Tinubu Ya Zare Sunayen Mutum Hudu Da Za a Ba Minista
A baya rahoto ya zo cewa Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya cire sunayen mutum huɗu daga cikin waɗanda zai ba muƙamin minista.
Shugaban ƙasar ya zare sunayensu domin samu ƙwararru da za su taya shi jan ragamar shugabancin ƙasar nan.
Asali: Legit.ng