An Samu Gwamnan APC Ya Yi Magana Game da Ministocin da Tinubu Ya Dauko
- Alhaji Umar Namadi ya ce Bola Ahmed Tinubu ya tuntube su wajen zakulo Ministocin tarayya
- A sakamakon haka, Gwamnan jihar Jigawa yana ganin ba za su samu matsala da shugaban kasa ba
- Gwamnatin Danmodi ta kuma yi alkawarin yin ayyukan da za su taimakawa mutanen Jigawa
Abuja - Gwamnan jihar Jigawa, Umar Namadi ya shaida cewa Gwamnonin jam’iyyar APC sun san halin da ake ciki kan batun nada ministoci.
Da ya yi hira da Daily Trust a garin Dutse, Gwamna Umar Namadi ya shaida cewa Bola Ahmed Tinubu ya tuntube su wajen zakulo ministocinsa.
Zuwa lokacin da za a fitar da sunayen wadanda za a ba mukamai a gwamnatin tarayyan, Gwamnan ya nuna ba za a samu wani sabani ba.
Gwamnoni sun san ya ake ciki
"Shakka babu, an tafi da Gwamnoni. Kwarai kuwa, an yi aiki da mu. ‘Yan Najeriya za su iya sa ran ganin sunayen da ba za su kawo rigima tsakaninmu ba."
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
- Umar Namadi
Gwamnan na APC da ya hau mulki kusan watanni biyu da suka wuce, bai yi dogon bayani a kan maganar ba, duk da jita-jita sun yi karfi sosai.
Minista daga jihar Jigawa
Legit.ng Hausa ta fahimci cewa Hon. Farouk Adamu Aliyu yana cikin wadanda ake tunanin zai iya zama Minista a gwamnatin tarayya daga Jigawa.
Tsohon ‘dan majalisar wakilan tarayyan ya nemi tikitin takarar Gwamnan jihar Jigawa a APC, amma bai yi nasara ba, Umar Namadi ya doke shi.
Ana tunanin jinkirin da aka yi wajen fitar da sunayen ministocin da za a tantance, ya ba Gwamnonin APC damar nuna tasirinsu a fadar shugaban kasa.
Mulki sai da lissafi
Hirar ba ta tsaya ga nadin mukamai a gwamnatin Bola Tinubu, an yi magana a kan Badaru Abubakar wanda ya yi Gwamna daga 2015 har zuwa 2023.
Danmodi kamar yadda aka fi sanin Gwamnan na Jigawa, ya ce abin da ake nufi da Mai Kalkuleta da tsohon Gwamnan shi ne lissafin dukiyar al’umma.
“Matsalar ita ce mutane su na juya asalin abin da kalkuleta ta ke nufi. Amfanin kalkuleta ita ce batar da dukiya da kyau, a san darajar kudi.
A tabbatar da duk sisin da aka kashe, an san inda ya shiga. Wannan gwamnati za ta yi koari wajen ganin tayi wa al’umma abin da ya dace.”
- Umar Namadi
Jackson Akpabio
A irin haka ne sai aka ji labari wani haimin Shugaban Majalisar Dattawa ya yi magana kan Ministocin Tarayya da ake sa ran nadawa a kasar.
Jackson Akpabio yana cikin wadanda su ka yi sa’ar ganin sunayen Ministocin bayan watanni biyu ana jira, ya ce sauran mutane za su ga jerin a yau.
Asali: Legit.ng