Na Ga Sunayensu: Hadimin Shugaban Majalisa a Kan Sababbin Ministocin Najeriya
- Jackson Akpabio ya tabbatar da cewa a ranar Alhamis, za a san wadanda za su iya zama Ministoci
- A matsayin Mai ba shugaban majalisa shawara, ya nuna ya ci karo da sunayen wadanda aka zakulo
- Akpabio ya yi karin haske ne bayan jita-jita sun yi yawa a kan mukaman, zuwa an jima kowa zai huta
Abuja - Jackson Akpabio wanda yana cikin masu taimakawa shugaban majalisar dattawa, ya ce a safiyar Alhamis za a ji sunayen Ministoci.
Dazu Punch ta rahoto Mista Jackson Akpabio yana nuna zuwa yau za a san hakikanin mutanen da za su zama sababbin Ministocin kasar.
Mai ba shugaban majalisar tarayyar shawara ya yi kira da jama’a su daina biyewa jita-jitar da ake yadawa dare da rana, wanda ba su tabbata ba.
A yau kowa zai ji sunayen
Da yake bayani a kan batun, Akpabio ya shaida cewa ya ga takardar sunayen wadanda za a tantance da nufin ba su kujera a gwamnatin tarayya.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
“Kamar dai sauran mutane, na ga jerin ni ma, sai mu jira zuwa gobe (yau). Mu daina hasashe, za a ga jerin a gobe (yau), za ku ga sunayen.”
-Jackson Akpabio
Ko da ya tabbatar da shi ma ya yi ido hudu da takardar nadin mukaman, hadimin shugaban majalisar bai iya kyankyasa abin da ya gano ba.
Abin da ya faru a Majalisa jiya
Da ake ta surutu cewa Godswill Akpabio da Jibrin Barau sun yi gaggawar barin majalisa a jiya, hadimin ya nuna ba wata matsala aka samu ba.
Jackson Akpabio yake cewa shugabannin majalisar sun bar zauren ne domin su duba aikin coci da ake yi, hakan bai da alaka da nadin Ministoci.
“Fitan shugaban majalisa da yammacin nan ba ta da alaka da sunayen Ministoci, ya je ne ya duba aikin coci da ake yi ginawa a majalisar.”
- Jackson Akpabio
Sabon jerin bogi ya fito
A wani sabon rade-radi, an ji cewa Andy Uba, Abubakar Kyari, Ben Ayade da Peter Orubebe duk su na cikin wadanda ake tunani za a dauko.
Ragowar su ne Dayo Adeyeye, Atiku Bagudu, Tanko Almakura, Oladimeji Bankole sai kuma Simon Lalong Ifeanyi Ugwanyi da Mal. Isa Yuguda.
Jita-jita sun kai intaha
Rahoton da mu ka fitar dazu ya nuna a dalilin dadewar da aka yi wajen nadin Ministocin, mutane na ta yada jita-jita a kafofin sadarwa.
Ana fitar da wasu sunaye a matsayin wadanda za a ba mukamai, sai dai duk ba su tabbata ba tukuna, a yau ake tsammanin maganar za ta kare.
Asali: Legit.ng