An Gama Komai, El-Rufai, Wike, Oyetola da Edun Za Su Zama Ministocin Bola Tinubu

An Gama Komai, El-Rufai, Wike, Oyetola da Edun Za Su Zama Ministocin Bola Tinubu

  • Watakila yau Shugaban majalisar dattawa zai karbi takardar shugaban kasa a game da nadin Ministoci
  • Bola Ahmed Tinubu zai dauko Minista daga kowace Jiha, sannan mutanen garin Abuja za su samu kujera
  • Ana tunani Shugaban kasar zai nada mutane 43 da zai yi aiki da su, mafi yawa da aka samu a shekarun nan

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Abuja - Idan abubuwa ba su canza a halin yanzu ba, an jima kadan Bola Ahmed Tinubu zai aikawa majalisar dattawa sunayen Ministocinsa.

Vanguard a rahoton da ta fitar dazu, ta ce shugaban Najeriyan ya zabi mutane 43 da yake so Sanatoci su tantance a matsayin Ministocin tarayya.

Daga cikin wadanda aka samu kishin-kishin cewa za a bada sunansu a yau akwai tsohon Gwamnan jihar Kaduna watau Malam Nasir El-Rufai.

Bola Tinubu
Bola Tinubu zai nada Ministoci Hoto: @Dolusegun
Asali: Twitter

Hadiman shugaban kasa zai koma FEC

Kara karanta wannan

An Samu Gwamnan APC Ya Yi Magana Game da Ministocin da Tinubu Ya Dauko

A jerin akwai Dele Alake wanda yanzu haka shi ne Mai ba shugaban kasa shawara a kan harkokin sadarwa, dabaru da sauran sha’ani na musamman.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Adegboyega Oyetola wanda ya rasa tazarce a zaben Osun zai samu shiga, akwai Wale Edun mai ba shugaba Bola Tinubu shawara kan tsare-tsaren kudi.

Ana rade-radin sunayen ministocin zai kunshi tsohon Gwamnan Ribas, Nyesom Wike.

Rahoton ya ce Adebayo Adelabu wanda ya yi mataimakin Gwamnan bankin CBN a baya da shugabar mata ta APC ta kasa, Dr. Beta Edu su na ciki.

Majalisar Ministoci za ta kara yawa

A wani kaulin kuma, yau shugaban kasar zai samu Ministoci 43 ne saboda wannan karo mutanen birnin tarayya Abuja za su samu wakilci a FEC.

Baya ga kowace jiha da za ta samu kujera, za a zabi karin Minista daga kowane yanki.

Kara karanta wannan

Za a Fito da Sunayen Ministoci, Gwamnoni da Tsofaffin Gwamnonin APC Sun Huro Wuta

Wata majiya ta ce idan ba a canza komai ba, za a ga sunan Sanatan gabashin Legas, Tokunbo Abiru, akasin rade-radin dawo da Olabode Agusto.

Idan an aika sunansa kuma aka yi nasarar tantance shi, ana tunanin Lateef Fagbemi, SAN zai zama Ministan shari’a kuma babban lauyan gwamnati.

Juyin mulki a makwabta

Duk da shugaban Najeriya ya yi kokarin aika dakaru zuwa Nijar, an ji labari sojoji sun yi juyin mulki, sun rufe ko ina tare da gargadin kasashen waje.

Sau hudu aka yi juyin mulki a wannan kasa ta yammacin Afrika daga shekarar 1960 zuwa yau. Wannan ne karo na biyar da aka kifar da farar hula.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng