Dalilin Da Yasa Dole Shugaba Tinubu Ya Bayyana Sunayen Ministocinsa Nan Da Ranar Juma'a
- Ranar Juma'a shi ne wa'adin ƙarshe da Shugaba Tinubu yake da shi na miƙa sunayen ministocinsa ga majalisar dattawa
- Sashi na 42 na kundin tsarin mulki ya yi tanadin cewa dole ne shugaban ƙasa da gwamonin su bayyana sunayen ministoci da kwamishinoni cikin kwanaki 60 da hawa mulki
- A ranar Juma'a, Shugaba Tinubu zai cika kwanaki 60 akan mulki bayan an rantsar da shi a ranar 29 ga watan Mayu
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Aso Villa, Abuja - Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu yana da sauran sa'o'i 48 ya miƙa sunayen ministocinsa ga majalisar dattawa domin tantancewa kamar yadda kundin tsarin mulki ya tanada, cewar rahoton Daily Trust.
Sashi na 42 na kundin tsarin mulki wanda aka yi wa garambawul, ya tilasta shugaban ƙasa da gwamnoni su naɗa ministoci da kwamishinoni cikin kwanaki 60 da hawansu kan mulki.
Shugaba Bola Tinubu zai cika kwanaki 60 a ranar Juma'a
A ranar Juma'a 28 ga watan Yuli, Shugaba Bola Tinubu zai cika kwanaki 60 akan karagar mulkin ƙasar nan.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Wannan jan ƙafar da shugaban ƙasar yake yi wajen bayyana sunayen ministocinsa, ya sanya jerin sunayen ministoci da dama sun yi ta yawo wanda har sai da gwamnati ta nesanta kan ta da su.
Shugaban masu rinjaye na majalisar dattawa ya bayyana cewa shugaban ƙasar zai aike da sunayen ministocinsa ranar Alhamis, rahoton Premium Times ya tabbatar.
A cikin ƴan kwanakinnan jerin sunayen ministoci da dama sun yi ta yawo a soshiyal midiya. A cikinsu akwai sunayen na kusa da Shugaba Tinubu da wasu tsaffin gwamnoni.
Sai dai, Dele Alake mai magana da yawun shugaban ƙasar ya yi watsi da batun cewa sunayen ministocin ya fita.
Matasa Sun Kutsa Katafaren Rumbun Ajiyar Kayayyaki Na Ɗan Majalisa, Sun Tafka Ta'adi, An Rasa Rayuka a Arewa
Jerin sunayen tsaffin gwamnonin da aka cire daga cikin sunayen ministocin Tinubu
A cikin jita-jitar da ake yaɗawa har da cewa wasu tsaffin gwamnoni da suka marawa Shugaba Tinubu baya a zaɓe, an cire sunayensu daga cikin ministocin.
Tsaffin gwamnonin sun haɗa da Nyesom Wike na jihar Rivers, Abdullahi Umar Ganduje na jihar Kano da Atiku Bagudu na jihar Kebbi.
Shugaba Tinubu Zai Mika Sunayen Ministocinsa Ranar Alhamis
Rahoto ya zo cewa shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu zai aike da sunayen ministocinsa ga majalisar dattawa ranar Alhamis.
Shugaban masu rinjaye na majalisar dattawa Sanata Bamidele shi ne ya bayyana cewa shugaban ƙasar ya tabbatar masa da hakan.
Asali: Legit.ng