Za a Fito da Sunayen Ministoci, Gwamnoni da Tsofaffin Gwamnonin APC Sun Huro Wuta
- Nan ba da dadewa ba ake sa ran za a sanar da wadanda ake so a ba kujerar Ministocin tarayya
- Tsofaffin Gwamnonin APC da su ka taimakawa Bola Tinubu a zaben shugaban kasa sun huro wuta
- ‘Yan APC na kokarin ba shugaban kasa ciwon kai game da wadanda zai ba mukamai a gwamnatinsa
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Abuja - Wasu tsofaffin da Gwamnoni masu-ci a jam’iyyar APC mai-mulki sun damu game da bata lokacin da aka yi wajen fitar da sunayen Ministoci.
Vanguard ta ce jagororin na APC sun matsawa Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu lamba a kan nadin Ministocin da a sanar da ‘yan awanni kadan.
A halin yanzu kwanaki uku su ka ragewa sabon shugaban Najeriyan, gwamnonin da su ka taimakawa APC a zaben da ya wuce su na so a tuna da su.
Gwamnoni sun bada sunaye 3
Sannan akwai Gwamnonin da ke kan mulki a jam’iyyar APC da ke son su samu ta-cewa game da wadanda za a zaba a matsayin Ministoci daga jihohinsu.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Rahoton ya ce wadannan Gwamnoni sun ba shugaban kasa sunayen kwararrun mutum uku da zai zaba su shiga majalisar zartarwa bayan tantance su.
Wata majiya a majalisar dattawa ta ce a safiyar Talata za a fito da sunayen wadanda aka zaba a matsayin Ministoci, sai a fara tantance su a ranar Alhamis.
Jihohin da za a gwabza
Wani da ya san abubuwan da ke faruwa, ya shaidawa jaridar cewa Bola Tinubu ya maida hankali a kan Ministocin da zai nada daga Ribas, Legas da Kano.
A matsayin mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima ya samu damar kawo sunayen wadanda za a ba kujerar Minista daga jihohin Arewa maso gabas.
A jihohi kamar Ribas, za a tada kura a kan nadin Nyesom Wike a matsayin Minista duk da ya na PDP. Babu mamaki FEC ta kunshi jiga-jigan PDP, LP da NNPP.
'Yan G5 za su samu Ministoci?
Ana ganin jigon na G5 ya ba Tinubu gudumuwa a takarar 2023, sai dai asalin ‘ya ‘yan jam’iyyar APC sun huro wuta cewa bai dace a manta da irin kokarin su ba.
Shi ma Gwamna Seyi Makinde zai kawo sunayen wadanda yake so a ba mukami a gwamnatin Tinubu, ko da ya na PDP, ya taimaki APC a babban zaben bana.
Doka ta wajabta nadin mukamai
Ana da labari cewa a cikin makon nan, dole za a san su wanene za su zama Ministocin Shugaba Bola Tinubu wanda ya dare kan mulki a watan Mayu.
Wajibi ne sabon shugaban kasa da Gwamnoni su fitar da sunayen Ministoci da kuma Kwamishinoninsu bayan 'yan Majalisa sun yi wa tsarin mulki garambawul.
Asali: Legit.ng