Yan Daba Sun Banka Wa Ofishin Kamfen Dan Takarar Gwamna a Jihar Kogi

Yan Daba Sun Banka Wa Ofishin Kamfen Dan Takarar Gwamna a Jihar Kogi

  • Yan bindiga da ake zaton yan daban siyasa ne sun ƙona ofishin kamfen jam'iyyar SDP da ke Lokoja, jihar Kogi
  • Rahoto ya nuna lamarin ya faru da tsakar dare lokacin da maharan suka lalata muhimman kayayyakin ofishin
  • Ɗan takarar mataimakin gwamna a inuwar SDP ya nuna rashin jin daɗinsa game da wannan harin da ya auku

Kogi state - Wasu ‘yan bindiga sun kona ofishin yakin neman zaben jam’iyyar Social Democratic Party (SDP) a Lokoja, babban birnin jihar Kogi.

Daily Trust ta tattaro cewa wasu da ake zargin ‘yan daban siyasa ne suka mamaye ofishin jam’iyyar da ke kusa da dandalin Paparanda a kan titin IBB a babban birnin jihar da tsakar dare.

Ofishin kamfen SDP a Lokoja.
Yan Daba Sun Banka Wa Ofishin Kamfen Dan Takarar Gwamna a Jihar Kogi Hoto: dailytrust
Asali: UGC

Shaidu sun ce maharan sun fatattaki jami’an tsaron da ke bakin aiki a ofishin yakin neman zaben, inda daga nan ne suka kona ofishin kamfen jam’iyyar.

Kara karanta wannan

'Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa da Wani Fitaccen Ƙwararren Likita Yana Kan Aiki a Arewacin Najeriya

Daga cikin abubuwan da maharan suka lalata yayin wannan hari har da kayayyaki masu daraja da takardu. An kuma kona motocin da ke cikin ofishin yakin neman zaben.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Maharan sun tafka ta'asa a Ofishin SDP

Ɗan takarar mataimakin gwamnan SDP a zaben gwamnan jihar da za a yi ranar 11 ga Nuwamba, Dakta Sam Ranti Abenemi ya ce:

"’Yan bindigar sun zo da yawa kuma suka cinna wa dukkan kadarorin da suka taras a ofishin wuta, wanda suka hada da janareto, kwamfutoci, kayan yakin neman zabe, da talabijin”.

Sai dai ya yi kira ga magoya bayan jam’iyyar da su kwantar da hankalinsu, yana mai jaddada cewa jam’iyyar za ta magance matsalar ta inda ya dace, Dailypost ta rahoto.

An san masu aikata wannan ɗanyen aikin - Adejoh Audu

A halin da ake ciki, Daraktan Sadarwa na ɗan takarar gwamnan SDP, Faruk Adejoh-Audu, ya ce

Kara karanta wannan

‘Yan Sandan Nasarawa Sun Bi Motar Da Aka Sace Daga Jihar Zuwa Taraba, Sun Kamo Mutane Biyu

“Muna kira ga duniya da dukkan masu hannu da shuni da su kawo agaji jihar Kogi ta hanyar yin Allah wadai da wadannan munanan ayyuka da ake ci gaba da yi na cin zarafi."
"Wannan al’amari na ci gaba da faruwa duk da yawan kuka da korafe-korafe da muka kai ga jami’an tsaro kan wadanda aka san su ke aikata wannan ta’addancin."

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sanda a jihar Kogi, SP William Aya, da aka tuntube shi kan lamarin, ya yi alkawarin nemo cikakken bayani ya dawo ga wakilinmu amma bai yi hakan ba har yanzu.

Majalisar Dokokin Jihar Kano Ta Amince da Karin Kwamishinoni Biyu

A wani rahoton Majalisar dokokin jihar Kano ta amince da naɗin karin kwamishinoni 2 da Abba Kabir Yusuf ya aiko mata.

Hakan ya biyo bayan nasarar tsallake matakin tantancewa da kwamishinonin biyu suka yi a zaman majalisa na ranar Litinin, 24 ga watan Yuli.

Kara karanta wannan

Na boye ya fito: Sojoji da DSS sun yi babban aiki, sun gano maboyar tsagerun 'yan tawaye a Najeriya

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262