Obasanjo Ya Ce Najeriya Ta Kunyata Kanta, Afrika Da Duniya Baki Daya

Obasanjo Ya Ce Najeriya Ta Kunyata Kanta, Afrika Da Duniya Baki Daya

  • Tsohon shugaban Najeriya Cif Olusegun Obasanjo ya ce Najeriya ta kunyata kanta da Afrika a idon duniya
  • Ya ce kasar ta gaza cimma muradunta tun bayan samun 'yanci shekaru 63 da suka gabata
  • Obasanjo ya ba da muhimman shawarwarin da ya kamata a bi don ganin an dawo da kasar kan turba

Abuja - Tsohon shugaban kasa Cif Olusegun Obasanjo, ya ce Najeriya ta kunyata kanta da kuma Afrika baki daya.

Ya bayyana hakan ne a yayin da yake jawabi wajen kaddamar da wani littafi da tsohon ministan masana'antu da zuba hannun jari, Olusegun Aganga ya rubuta kamar yadda The Punch ta wallafa.

Obasanjo ya ce Najeriya ta kunyata Afrika
Obasanjo ya ce Najeriya ta bai wa kanta da Afrika kunya a idon duniya. Hoto: Zara Onyinye
Asali: Facebook

Najeriya ta gaza cimma muradunta tun bayan samun 'yanci

Obasanjo ya ce Najeriya ta gaza cimma muradunta tun bayan samun 'yancinta shekaru 63 da suka gabata, inda ya ce ta kunyata Afrika ma ba iya kanta kadai ba.

Kara karanta wannan

Yadda Marigayi Albani Ya Hango Janye Tallafin Man Fetur Shekaru 9 da Suka Wuce

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shugaba Tinubu ne ya kaddamar da littafin ta hannun mai ba shi shawara na musamman kan tsare-tsaren harkokin kudi, Olawale Edun.

Taron ya samu halartar manyan Najeriya da dama da suka kunshi tsofaffin shugabanni da masu ci a yanzu.

Obasanjo ya bayar da muhimman shawarwari a wajen taron

Obasanjo wanda ya halarci taron ta manhajar taro ta zamani, ya bayar da muhimman shawarwarin da za su taimaka kasar ta ci gaba.

Daga cikin abubuwan da ya yi magana a kansu akwai maganar tsaro da zaman lafiya, wadanda ya ce ba za a iya samunsu ba har sai an tabbatar da adalci a kasa.

Haka nan ya ce barin sama da yara miliyan 20 na gararamba a kan titi ba tare da zuwa makaranta ba kalubale ne babba da ya zama dole a magance shi in ana so a ci gaba.

Kara karanta wannan

Da Saura: Malam Idris Zai Ci Gaba da Zamaan Gidan Kaso Saboda Dalilai Na Beli

Obasanjo ya kuma ba da shawarar cewa dole ne a samar da cibiyoyin horar da matasa kan sana'o'i da sanin makamar aiki, wanda hakan zai yi matukar taimakawa matsalar tsaron da ta yi wa kasa katutu.

A rahoton Daily Trust, Obasanjo ya ce duk da ana zuwa da sabbin tsaruka masu kyawu, ya zama wajibi a rika lura da yadda ake aiwatar da su don gudun jefa 'yan kasa cikin talauci.

Kotu ta nemi Buhari, Jonathan, Yar'adua da Obasanjo ba da bayani kan kudaden Abacha

Legit.ng a baya ta kawo rahoton wata babbar kotun tarayya da ke Abuja da ta bukaci tsofaffin shugabannin Najeriya hudu bayar da bahasin yadda suka kashe dala biliyan biyar ta Abacha.

Kotun ta bukaci Tinubu ya ba da bayanai kan yadda Buhari, Jonathan, Yar'adua da Obasanjo suka kashe kudaden da kuma wuraren da aka kashe su.

Asali: Legit.ng

Authors:
Deen Dabai avatar

Deen Dabai Zaharaddeen Hamisu marubuci kuma ma'aikacin jarida ne da ke da gogewa wajen iya tantance sahihan labarai da na karya. Ya yi digirinsa a jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Baya ga haka, ya shafe sama da shekaru 5 a bangaren aikin watsa labarai wanda hakan ya bashi gogewa ta musamman a aikin jarida. Za a iya tuntubarsa ta adireshinsa na yanar gizo: deen.dabai@corp.legit.ng